Dubban manoma sun yi zanga-zanga a India

Farmers have walked for six days to reach Mumbai Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Farmers have walked for six days to reach Mumbai

Sama da manoma dubu talatin sun hadu a babban birnin kasar Indiya, Mumbai, bayan tattakin sama da kilomita 167 daga yankin Nashik don neman rancen da sayen amfanin gonarsu cikin farashi mai kyau.

Manoman da suka yi gangamin, wadanda suka hada da yara da mata da tsofaffi, sun ce gwamnati ba ta aiwatar da tallafin bashin kudaden da ta yi alkawari za ta yi a bara.

Gwamnatin jihar Maharashtra ta yadda da tattaunawa don kawo karshen zanga-zangar.

Manoman sun ce jihar ta samu ci gaba sosai amma ba ta yi musu abin a-zo-a-gani.

Dandazon manoman ya yi kwanaki shida suna takawa daga Nashik, sannan suka sa lokacin da za su isa filin Azad Maidan da ke Mumbai, inda aka saba gudanar da manyan taruka da zanga-zanga, da safiyar Litinin domin kada su hana gudanar da jarrabawar makarantu, da hana ma'aikata zuwa aiki.

Manoman sun ce suna so a biya su akalla daya da rabin kudin amfanin gonakinsu.

Suna kuma son kungiyoyin manoma, wadanda suka fi noma a cikin daji, su samu damar mallakar gona.

Manoman suna shirin yin sansani a wurin har sai gwamnati ta amince da biyan bukatunsu.

Shugaban manoman Vijay Javandhia ya shaida wa BBC Marathi cewa "aikin noma ya ragu sosai a kasar. Yawan kudin da ake samu a cikin auduga da hatsi yana raguwa kulli yaumin"

Hakkin mallakar hoto BBC Marathi
Image caption Many women are also participating in the march

Sakhubai, wata tsohuwar manomiya mai shekaru sittin da biyar daga Nashik, ta ce "muna bukatar filinmu kuma wannan ita ce bukatarmu na farko".

"Na ji ciwo a kafafuna saboda tafiya mai yawa, amma zan ci gaba da nuna rashin amincewa har sai an biya mana bukatunmu," in ji ta.

Labarai masu alaka