Jirgi ya yi hatsari a filinsa da ke Kathmandu

Photo showing smoke rising from the airport runway Hakkin mallakar hoto Twitter/@Bishnusapkota

Wani jirgi ya fadi a filin jirgin sama na Tribhuvan, babban birnin Kathmandu na kasar Nepal, in ji jami'ai.

Jirgin saman na Bangladash, mallakin kamfanin Amurka-Bangla, ya kauce daga kan titin jirgin sama yayin da yake sauka ranar Litinin, inda ya haddasar da gobara da ma'aikatan kashe gobara ke ta kokarin kashewa.

Jami'ai sun shaida wa BBC cewa kimanin fasinjoji sittin da bakwai ne ake zaton suna jirgin. Ba a tabbattar da yawan wadanda suka mutu ba.

Hukumai sun ce an ceto mutane goma sha bakwai a yanzu.

Hotuna da bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zamani sun nuna hayaki yana tashi daga filin jirgin saman.

Kafofin watsa labarai na gida sun bayyana jirgin saman da cewa kirar S2-AGU, Bombardier Dash 8 Q400 ne, amma jami'ai ba su tabbatar da hakan ba.

Jirgin ya sauka a filin jiragen sama na TIA, wanda aka fi sani da Kathmandu International Airport, da karfe biyu da minti ashirin na kasar, a cewar wani shafin intanet mai gano inda jirgin saman yake zuwa, FlightRadar24.

Labarai masu alaka