An hana sa anko da kida a taron biki a Nijar

Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan kade-kade da shagulgula a bukukuwa a Nijar

Masarautar Abzin da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar ta hana wasu dabi'u da suka hada da anko da hana kade-kade yayin bukuwan aure ko suna.

Sai dai mazauna Agadez din cewa suke son barka da wannan mataki.

Matakin na mai martaba Sarkin Abzin na ci gaba da samun martini daga mazauna garin na Agadez da suka ce su dama sun dade suna jiran irin wannan mataki.

Matan da sune dokar hana anko ta shafa sun ce za mu ce ta tadda mu je, sun kuma koka game da da ayarin da ake yayin kai amarya alokutan bikin.

Wata mata Malama Gaisha ta shaida wa BBC cewa, dama uwaye mata ne suke shan wahalar sayen anko a lokutan biki.

"Muna neman abin da za mu kai bakin salati amma sai batun anko ya daga mana hankali don yara suna sa mu a gaba sai mun saya musu.

Shi ma Mallam Mohamed wani uba ne a garin na Agadez, ya kuma jinjinawa mai martaba Sarkin Abzin kan wannan doka ta hana anko da ayarin motocin kai amarya da kide-kide ranar aure ko suna da dai sauran su.

Dalilin daukar matakin

Sakataren fadar Sarkin Abzin ya ace an dauki matakan ne saboda yadda koke-koke suka yi yawa daga al'umma.

"Malamai daga unguwanni daban-daban suka jawo hankalinmu saboda yadda jama'a ke kai kuka wajensu don ganin an dauki mataki.

"Shi kansa Sarki ana yawan koka masa, shi ya sa aka ga ya dace a dauki matakan."

A yanzu an sa ido don ganin ko wannan doka zata dore ko kuwa ta dan lokaci ce za ta shude kamar yadda aka saba gani a sauran masarautu da suka dauki iri wannan doka a baya.

Labarai masu alaka