Masu teba na karuwa a Qatar

Akwai masu teba da dama a Qatar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai masu teba da dama a Qatar

Qatar za ta zamo kasa ta farko a duniya da za a fara gwajin mutane a kan cutar ciwon siga nau'i na biyu.

Kusan mutum guda a cikin mutum biyar a kasashen yankin Gulf, na fama da wannan cuta wanda adadin ya ninka sau biyu a kan kason da ake da shi a duniya.

Cutar ciwon siga na daya daga cikin manyan cututtukan da suke sauran hallaka mutane a kasar.

Cutar na janyo adadin sigan da ke jikin mutum ya yi sama, sannan ta kan haifar da karuwar hadarin kamuwa da cutar shanyewar barin jiki da ciwon zuciya.

Ta na kuma daya daga cikin cutukan da suke haddasa makanta.

Wannan dalilai ya sa ma'aikatar lafiya ta kasar ta shaida wa BBC shirinta na fara gwada duk wasu 'yan kasar da suka jima a duniya a kan wannan cuta kafin karshen shekarar da muke ciki.

Wannan ne dai karon farko da wata kasa za ta fara irin wannan gwaji a duniya.

Kazalika wannna mataki wani bangare ne na yakin da gwamnatin kasar ta Qatar ke yi kan yawan teba wadda ke haddasa kamuwa da cutar ciwon sigan.

Fiye da kaso 70 cikin 100 na al'ummar kasar, suna da kiba ko kuma teba.

Farfesa Abdul Badi Abou Samra, mamba ne a kwamitin da ke kula da masu teba a Qatar, ya ce suna so su rage yawan masu kamuwa da wannan cuta, shi ya sa ma za a bullo da haraji a kan sikari da sauran kayayyaki, sannan a tabbatar da ana rubuta bayanan kayayyaki da abin da ya kunsa.

Labarai masu alaka