Mutum 38 sun mutu a hatsarin mota a Habasha

Map of Ethiopia

Jami'ai sun ce mutum 38 ne suka mutu a Habasha bayan da motar bas da suke yin buolaguro a ciki ta rufto daga kan wata gasa.

Hatsarin ya faru ne a gundumar Amhara da ke arewacin Addis Ababa babban birnin kasar.

Jami'ai a yankin sun tabbatar da mutuwar maza 28 da mata 10.

Kafar yada labaran Fana ta ruwaito cewar fasinjoji 10 ne suka rayu amma sun ji munanan raunuka.

Ta kara da cewa mafi yawan wadanda hatsarin ya rutsa da su daliban jami'a ne.

Wata kafar yada labarai mai zaman kanta ta kasar Addis Standard, ta ce motar ta fado ne daga nisan mita biyar.

Kasar Habasha dai wadda tana daya daga cikin kasashen Afirka da tattalin arzikinsu ke habaka, ta fadada da kuma gyara titunanta a shekarun baya-bayan nan.

Mutane da dama sun fi amfani da motocin bas na safa don yin doguwar tafiya.

Labarai masu alaka

Labaran BBC