Buhari ya yi watsi da bukatar sauya dokar zabe

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hon Kawu Sumaila ya yi karin bayani kan dalilan da suka sa Buhari ya yi watsi da kudurin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi fatali da bukatar sauya dokokin zabe, kudirin da tuni ya samu amincewar zauren majalisun tarayya guda biyu.

Hon Kawu Sumaila mai bai wa shugaban shawara kan harakokin majalisa ya tabbatar wa da BBC cewa shugaban ya yi watsi da kudirin.

Kudirin wanda ya shafi sauya dokokin zaben Najeriya, ya shafi fara gudanar da zaben 'yan Majalisar Tarayya kafin na shugaban kasa.

Buhari ya aika wa da zauren majalisun guda biyu wasika da ke kunshe da bayani kan dalilin yin watsi da bukatar sauya dokokin zaben.

A cikin wasikar, Buhari ya ce kudirin ya saba wa 'yancin INEC hukumar zabe mai zaman kanta da ke da alhakin shiryawa da gudanar da zaben, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Majalisun dokokin dai sun ce sun sauya fasalin tsarin zaben 2019 ne domin Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya samu damar sanya ido a zabukan.

Sai dai tun a lokacin wasu 'yan kasar sun soke su kan hakan, suna masu cewa matakin tamkar wata dama ce ga 'yan majalisar su lashe nasu zaben sannan su yi watsi da shugaban kasa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Buhari ya ce sauya dokar zabe ya saba wa 'yancin hukumar Zabe

Labarai masu alaka