An daure masu sayar da magungunan jabu a Benin

Ana yawan samun kayayyakin jabu a Benin ciki har da magunguna Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yawan samun kayayyakin jabu a Benin ciki har da magunguna

Wata kotu a Benin ta daure wasu shugabannin kamfanonin hada magunguna su bakwai inda ake tuhumarsu da sayar da magungunan jabu.

An dauki wannan mataki ne a wani bangare na yakin da gwamnatin kasar ke yi a kan shigo ko sayar da jabun magunguna.

Mutanen bakwai na yiwa wasu dillalai masu shigo da magunguna aiki ne ta hanyar dillancin magunguna kama daga maganin rage radadi zuwa maganin zazzabin cizon sauro wanda ake sayarwa a kasar da kewaye.

An dai daure su ne na tsawon shekara hudu a gidan kaso, tare da tarar CFA miliyan 100, kwatankwacin dala dubu 190.

Yayin da wasu mutum biyu kuma aka yanke musu zaman gidan kason na tsawon wata shida.

A kance magani ya zama na jabu idan ya rasa wani sinadari ko kuma yawan sinadarin bai kai yawan da ya kamata ba.

Kuma a kan sayar da irin wadannan magungunan a cikin fakitin da ya yi kama da na gaske.

Kwatanou dai na daga cikin garuruwan kasashen yammacin Afirka da suke da babbar tashar jirgin ruwa.

A shekarar da ta gabata, 'yan sanda a Benin sun kai samame kan shagunan da ke sayar da magungunan jabu.

Kasar dai na son ta dawo da kimar ta ne, saboda kallon da ake mata a matsayin wata kasa da ake sayar da jabun kayayyaki.

Labarai masu alaka