Majalisar Dinkin Duniya ta karrama Rahama Sadau

rahama sadau Hakkin mallakar hoto Rahama Sadau

An karrama jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood ta arewacin Najeriya Rahama Sadau, a wurin bikin ba da lambar yabo ta jaruman fina-finai mata Women Illuminated Film Festival, wanda aka yi a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya.

Jarumar ta wallafa hotunan bikin bayar da kyautukan da aka yi a birnin New York a ranar Litinin a shafinta na Instagram, tana mai nuna matukar jin dadinta.

Rahama ta rubuta cewa: "Wannan girmamawa ce babba a gare ni, na ji dadi matuka, kuma ina alfaharin kasancewa a wannan daren tare da hazikan mata da dama."

Ta kara da cewa: "Akwai wadansu lokuta a rayuwa da ya kamata mutum ya tsaya ya tambayi kansa, yaya aka yi ma na kawo nan? Babu ko tantama wannan na cikin irin wadannan lokutan wadanda har abada ba zan taba mantawa da su ba."

Abokan aikin Rahama da dama sun taya ta murna a shafukan sada zumunta kan wannan lambar yabo da ta samu.

Jarumi Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa: "Ina taya ki murna 'yar uwata."

Ana yin wannan bikin na ba da lambar yabo ta jaruman fina-finai mata ne tare da hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya don nuna martaba mata masu yin fim, da kuma nuna gajerun shirye-shirye.

Rahama Sadau dai a baya an sha samun ce-ce-ku-ce a kanta a masana'antar Kannywood, inda har a bara aka dakatar da ita sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.

Sai dai a watan Oktobar da ya gabata ne jarumar ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon abun da tayi.

Labarai masu alaka