Najeriya: Shugaba Buhari ya kai ziyara Dapchi

Shugaba Buhari a Damaturu Hakkin mallakar hoto @BashirAhmaad
Image caption Gwamnatin Yobe ta tarbi Shugaba Buhari a Damaturu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar, inda aka sace 'yan matan sakandare fiye da 100 a watan da ya gabata.

Shugaban ya gana da iyayen yaran da aka sace a makarantar sakandaren, inda a nan ne aka sace 'yan matan.

Gwamnati ta sha suka kan yadda ta tunkari sace 'yan makarantar, wanda aka hora alhakinsa kan kungiyar Boko Haram.

Ziyarar wani bangare ne na rangadin da ya ke yi a jihohin da ke fama da rikice-rikice a kasar.

Tun da safiyar Larabar ne Shugaba Buhari ya isa Damaturu, babban birnin jihar Yobe inda gana da shugabannin al'umma da sarakunan gargajiya.

Tuni dai iyaye a garin Dapchi suka yi dafifi a makarantar da aka sace 'ya'yan nasu inda suke jiran isar Shugaba Buharin don ganawa da su.

Kalaman Buhari ga 'yan Dapchi

  • Shugaban ya isa garin Dapchi da akalla jirage ma su saukar Angulu shida
  • Ya tattauna da iyayen 'yan mata 110 da aka sace a Dapchi
  • Ya amsa cewa akwai sakacin jami'an tsaro
  • Gwamnatinsa na iya kokarinta domin sako 'yan matan
  • Ya bukaci iyayen su kara yin hakuri.

Wani daga cikin iyayen yaran ya shaida wa BBC cewa: "Muna jira ne shugaban ya zo ya gamsar da mutanen gari kan kokarin da gwamnati ke yi na ceto 'ya'yansu da kuma matakan da za a dauka don hana sake afkuwar irin hakan."

Martanin iyayen 'yan matan

Amma wasu daga cikin iyayen 'yan matan sun shaida wa BBC cewa babu tabbas ga kalaman shugaban.

Wasu da dama daga cikinsu sun bayyana damuwa kan matakan da gwamnati ke dauka musamman bayan da aka kai harin.

Daya daga cikin iyayen da aka tafi da 'yayanta guda biyu ta ce ta yi mamakin yawan jami'an tsaron da suka rako shugaban.

Ta ce: "Shin ina sojojin suka shiga a lokacin da aka sace 'yayansu?"

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Shugaba Buhari ya gana da shugabannin al'umma a Damaturu

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata sama da 100 daga makarantar sakandaren Dapchin kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Sace 'yan matan na Dapchi, wanda ya zo shekara hudu bayan sace 'yan matan Chibok, ya tayar da hankalin mazauna garin da ma jihar baki daya.

Kuma ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke cewa ta karya lagon mayakan na Boko Haram.

A ranar Litinin ne tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce kasarsa na aiki tare da Najeriya domin ganin an kubutar da 'yan matan.

Shi dai Shugaba Buhari ya ce ba ya so a yi amfani da karfin tuwo domin kada a jefa rayukan yaran cikin hadari, a don haka a shirye yake ya tattauna da wadanda suka sace su.

A baya dai gwamnatinsa ta yi musayar mayakan Boko Haram da wasu daga cikin 'yan matan Chibok.

Labarai masu alaka