Wani kare ya mutu a cikin jirgi a Amurka

Overhead locker. File photo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin jirgi na United ya ce ba a sa dabbobi a lokar cikin jirgi

Kamfanin jiragen sama na United ya amsa "laifinsa" a kan mutuwar da wani kare ya yi a jirgi bayan wata ma'aikaciyar cikin jirgi ta sa a dora karen a lokar da ake sa kaya ta cikin jirgin.

Kamfanin jirgin saman ya ce "wannan wani mummunan hatsari ne da bai taba faruwa ba."

Karen mai wanda jinsin karnukan Faransa ne, ya mutu a lokacin da jirgin ke tashi daga jihar Houston zuwa New York a ranar Litinin.

Shaidu sun ce ma'aikaciyar cikin jirgin ta cewa daya daga cikin fasinjojin ta sa jakar da karenta ke ciki a cikin loka.

Daga baya kuma ta ce ita ba ta san cewa karen yana cikin jakar ba.

A wata sanarwa da kamfanin jiragen United din ya fitar ya ce: "Mun dauki laifin wannan mummunan abu da ya faru kuma mu na nuna matukar nadamarmu tare da mika jajenmu ga masu karen."

Sanarwar ta kara da cewa: "Muna bincike sosai kan abin da ya faru don kada irin haka ya sake faruwa, kuma bai kamata a taba sanya dabba a cikin lokar cikin jirgi ba."

Wata fasinja Maggie Gremminger, wadda ta ce ta zauna a bayan mata mai karen, ta bayar da labarin abun da ya faru.

Ta shaidawa wani shafin yanar gizo na tafiye-tafiye cewa "Na ga wata ma'aikaciyar cikin jirgi ta cewa wata mata ta sanya jakarta a lokar cikin jirgi.

"Sai fasinjar ta ja baya tana cewa ba za ta sa jakar a loka ba don karenta na cikin jakar."

"Ma'aikaciyar jirgin ta ki ji ta dunga gaya wa fasinjar dole ta sa jakar a loka, inda a karshe dai waccar din ta sa.

"Bayan jirgin ya sauka, karen ya riga ya mutu, sai matar ta fadi kasa ta dinga kuka."

Shaidu sun yi ta rubutawa a shafin sada zumunta na Twitter cewa zuciyarsu ta kare.

Ko da yake, ana samun iska kadan na shiga ta lokan, amma duk da haka rashin isasshiyar iska zai iya haifar da mutuwar kare, in ji Rahoton kafofin watsa labarai na Amurka.

Manufofin Majalisar Dinkin Amurka a kan tu'ammali da dabbobi a cikin jirgi shi ne "dole ne a sa dabba a cikin wata jaka da za ta iya shiga lokar cikin jirgin."

"Jakar sai ta yi cif-cif a karkashin kujerar fasinjan da ke gaba, kuma dole jakar ta kasance a nan a ko da yaushe."

Labarai masu alaka