Bidiyon matar da ke fentin gidaje a Abuja

Bidiyon matar da ke fentin gidaje a Abuja

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon yadda Lariyat ke aikinta:

Wata sana'a da aka fi sanin maza da yi ita ce sana'ar yin fenti, amma a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, an samu wata mace da take sana'ar hadawa da kuma yi wa gine-gine fenti.

Lariat ta ce ta fara wannan sana'a ce tun a shekarar 2009, inda a yanzu haka take da kamfanin hada fenti da kuma dumbin ma'aikata.

Ta shaida wa BBC cewa ta shiga sana'ar ce a lokacin da take neman kudin da za ta yi jari don fadada sana'arta ta sayar da kayan ciye-ciye.