Dan majalisar da ya ce a mari mata ya nemi afuwa

Mr Twinamasiko, ya ce ba laifi ba ne miji ya daki matarsa matukar bai ji mata rauni ba Hakkin mallakar hoto NTV
Image caption Mr Twinamasiko, ya ce ba laifi ba ne miji ya daki matarsa matukar bai ji mata rauni ba

Wani dan majalisar dokoki a Uganda wanda kafafan yada labaran kasar suka rawaito shi a makon jiya yana cewa, ba laifi ba ne idan miji ya mari matarsa domin ladabtarwa, ya nemi afuwa.

A cikin wata sanarwa da dan majalisar, Onesmus Twinamasiko, ya fitar ya bukaci takwarorinsa 'yan majalisar da kuma al'ummar kasar ta Uganda da su yafe masa bisa kalaman da ya yi.

Mr Twinamasiko, ya ce kalaman na sa ba wai suna nufin a rinka cin zarafin mata ba ne, shi kansa yana daraja mata matuka gaya, kuma ba ya goyon bayan a ci zarafi kowacce mace.

Ko da ya ke dan majalisar, ya shaida wa BBC cewa, ya taba marin matarsa akalla sau daya.

Mr Twinamasiko, ya ce dan mutum ya mari matarsa ba laifi bane matukar ba ji mata rauni ba.

Wadannan kalaman nasa dai sun janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta na kasar, inda wasu ke alawadai da kalaman na sa na marin mace.

Labarai masu alaka