Libya na zargin mutum 205 da fasa kaurin mutane

Ana yawan samun fasa kaurin mutane a Libya, musamman 'yanci rani da ke kokarin tsallaka wa turai ta kasar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana yawan samun fasa kaurin mutane a Libya, musamman 'yanci rani da ke kokarin tsallaka wa turai ta kasar

Kasar Libya ta bayar da sammacin kama wasu 'yan kasar da kuma wasu 'yan kasashen waje 205, wadanda ake zargi da hannu a fasa kaurin mutanen da suke kokarin tsallaka wa turai.

Ana dai zargin mutanen ne da fasa kaurin mutane da azabtar da su da kisa da kuma fyade.

Ofishin ministan shari'a na Libya, ya ce mutanen sun hadar da jami'an tsaron kasar da jami'an da ke kula da wuraren tsare masu tafiya ci rani da kuma jami'an ofishin jakadancin kasashen Afirka da ke Libya.

Kasar Libya dai na cikin tashin hankali tun bayan hambarar da gwamnatin shugaban Mua'ammar Gaddafi, a shekarar 2011.

An kuma raba mulkin kasar ne tsakanin masu tayar da kayar baya daban-daban da kuma gwamnatoci biyu da ke hamayya da juna, wanda hakan ya bayar da damar ci gaba da aiwatar da abubuwan da basu dace ba a kasar.

Kazalika kasar ta zamo wata hanya da dubban mutane daga kasashen kudu da hamadar sahara ke kokarin tsallaka wa turai ta ruwa.

An gudanar da bincike a kan mutanen ne tare da hadin gwiwar ofishin mai shigar da kara na Italiya, bayan da aka kafa wani kwamitin jami'an tsaro da jami'an leken asiri a tsakanin kasashen biyu wato Libya da Italiya.

Babban darakta a ofishin ministan sharia'ar na Libya, Seddik al-Sour, ya ce an samu jami'an hukumar shige da ficen a cikin wannan badakala.

Labarai masu alaka