'Makiyaya sun bude wa ayarin sojoji wuta a Plateau'

Rikici tsakanin manoma da makiyaya yana kara kamari a wasu sassan Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rikici tsakanin manoma da makiyaya yana kara kamari a wasu sassan Najeriya

Dakarun shiyya ta uku na rundunar sojin Najeriya da ke jihar Filato a yankin tsakiyar kasar, sun kama wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu a rikicin da aka yi tsakanin al'ummar Miango da Makiyaya a ranar Laraba a kauyen Rafiki.

Mai magana da yawun sojin Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu ya ce dakarun sun kuma kwace makamai da dama daga hannun mutanen.

Dakarun sun je kauyen ne don kai wa mutanen yankin dauki sakamakon rikicin da ya barke wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla 23.

Janar Chukwu ya ce a yayin da dakarun suke kokarin kwantar da tarzomar ne sai makiyaya suka bude wa ayarin motocinsu wuta, inda suka kashe sojoji biyu.

"Wannan al'amari ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu. Amma tuni aka kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a rikice-rikicen,' a cewarsa.

Ya kara da cewa a yayin da suke bincike, sojojin sun gano gawarwakin fararen hula 23 da suka mutu a garin Mararaba Dare wanda ke kusa da kauyen Rafiki, kuma wasu da dama sun jikkata.

"Kazalika sojojinmu biyu sun ji rauni a wannan kauye, amma ana duba lafiyarsu a asibitin sojoji da ke Shiyya ta Uku, kuma suna samun sauki," in ji sanarwar da sojin suka fitar.

Daga cikin makaman da aka kama har da bindiga samfurin Ak 47 guda daya da kuma harsasai da dama.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaron Najeriya sun sha alwashin kawo karshen rikice-rikicen

Rundunar ta kara da cewa a yanzu haka dai dakarun sun kara wuraren da suke sunturi don ganin rikicin bai sake barkewa ba.

Jihar Filato dai na daga cikin jihohin da ke fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini.

Ko a farkon wannan makon ma an samu rahotannin rikici tsakanin al'ummun karamar hukumar Bassa ta jihar da kuma na karamar hukumar Kauru da ke makwabciyarta a jihar Kaduna.