Mutum takwas sun mutu a hatsarin jirgin soji a Senegal

A Senegalese soldier looks at the wreckage of the Convair plane chartered jointly by the French tour operator Club Mediterranee and Air Senegal which crashed in Senegal's southern Casamance region 09 February 1992, killing 24 of the plane's 50 passengers and all six crew members. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar 1992 ma an yi wani mummunan hatsarin jirgi a senegal inda mutum 24 suka mutu

Wani jirgin Soji ya yi hadari a kasar Senegal, dauke da fasinjoji 20 a ciki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum bakwai sun ji rauni, yayin da aka nemi sauran mutum 13 aka rasa.

Jirgin dai ya fadi ne a dajin Mangrove da ke kudu maso gabashin yankin Missarah.

Wasu masu kwale-kwale ne suka kubutar da mutum bakwai din da suka jikkata.

Tuni kuma shugaban kasar Macky Sall ya aike da wata tawaga don binciko wadanda suka bata, kuma kawo yanzu ba a fadi musabbabin hadarin jirgin ba.

Mista Sall ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan da kuma jajanta wa wadanda suka ji rauni.

Rabon da a yi hatsarin jirgin sama a Senegal tun 2015, a lokacin da mutum bakwai suka mutu a wani hatsari.

Labarai masu alaka