Me ya sa zuwan Buhari Dapchi bai burge wasu 'yan Najeriya ba?

Buhari a Dapchi Hakkin mallakar hoto @BashirAhmaad

An shafe kusan wata guda kafin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kai ziyara garin Dapchi - inda mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan makarantar sakandare 110.

Amma kamar yadda muka ruwaito a ranar Laraba, a karshe ya kai ziyarar da aka jima ana sa ran yin ta.

Sai dai ga dukkan alamu ziyarar ba ta burge mafi yawan iyayen yaran da ma wasu ma'abota shafukan sada zumunta a kasar ba.

Wasu sun yi korafi bayan da hotunan yadda ziyarar ta kasance suka yi ta yaduwa a intanet inda aka ga irin tawagar da shugaban ya je da ita da kuma jar dardumar da aka shimfida masa a lokacin da ya isa.

Hakkin mallakar hoto FamousBlog Instagram

Sai dai a bangare guda kuma, wasu 'yan Najeriyar na ganin cewa shugaban ya yi matukar kokari wajen yin wannan ziyara.

Suna cewa ba za a taba kwatantawa da abun da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya yi ba, kan sace 'yan matan Chibok fiye da 200 ba a lokacin da yake mulki, ba tare da ya ziyarci garin ba.

Shugaba Buhari - wanda ya yi alkawarin cewa: "ba za a huta ba" har sai an gano 'yan matan, ya isa garin Dapchi karkashin rakiyar jirage masu saukar ungulu shida don ganawa da dalibai da iyayensu da malamansu.

Martanin iyayen 'yan matan

Amma wasu daga cikin iyayen 'yan matan sun shaida wa BBC cewa babu tabbas game da kalaman shugaban.

Wasu da dama daga cikinsu sun bayyana damuwa kan matakan da gwamnati ke dauka musamman bayan da aka kai harin.

Daya daga cikin iyayen da aka tafi da 'yayanta guda biyu ta ce ta yi mamakin yawan jami'an tsaron da suka rako shugaban.

Ta ce: "Shin ina sojojin suka shiga a lokacin da aka sace 'yayansu?"

Su kuwa masu amfani da shafukan sada zumunta sun kasa dauke idonsu daga jar dardumar....

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Abun da masu amfani da shafukan sada zumunta ke fada

Kalaman Buhari ga 'yan Dapchi

  • Shugaban ya isa garin Dapchi da akalla jirage ma su saukar Angulu shida
  • Ya tattauna da iyayen 'yan mata 110 da aka sace a Dapchi
  • Ya amsa cewa akwai sakacin jami'an tsaro
  • Gwamnatinsa na iya kokarinta domin sako 'yan matan
  • Ya bukaci iyayen su kara yin hakuri.

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata sama da 100 daga makarantar sakandaren Dapchin kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Sace 'yan matan na Dapchi, wanda ya zo shekara hudu bayan sace 'yan matan Chibok, ya tayar da hankalin mazauna garin da ma jihar baki daya.

Kuma ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke cewa ta karya lagon mayakan na Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Shugaba Buhari ya gana da shugabannin al'umma a Damaturu

A ranar Litinin ne tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce kasarsa na aiki tare da Najeriya domin ganin an kubutar da 'yan matan.

Shi dai Shugaba Buhari ya ce ba ya so a yi amfani da karfin tuwo domin kada a jefa rayukan yaran cikin hadari, a don haka a shirye yake ya tattauna da wadanda suka sace su.

A baya dai gwamnatinsa ta yi musayar mayakan Boko Haram da wasu daga cikin 'yan matan Chibok.

Labarai masu alaka