Amurka: Rasha na fuskantar sabbin jerin takunkumi

Yevgeny Prighozin, wani attajiri mai alaka ta kut-da-kut da fadar Kremlin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yevgeny Prighozin, ya musanta tuhumar da Amurka ke masa

Ma'aikatar Kudi ta Amurka ta sakawa kamfanoni biyar na kasar Rasha da kuma wasu mutum 19 'yan kasar ta Rasha.

Amurka na tuhumarsu da hannu a kutsen da aka yi wa wasu kamfanoni da hukumomin kasar, da kuma yin katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016.

Sakataren ma'aikatar kudi na Amurka, Steve Mnuchin ya ce gwamnatin Amurka ta yi imanin mutanen na da hannu wajen kutsen da Rasha ta yi wa zaben Amurka a shekarar 2016.

Ta ce kuma mutanen sun janyo asarar biliyoyin daloli a sanadiyyar wani kutse da aka yi wa wasu hukumomin kasar a watan jiya.

A cikin mutanen, da akwai Yevgeny Prighozin, wani attajiri da ya mallaki jerin gidajen abinci a Rasha, kuma mai alaka ta kut-da-kut da fadar Kremlin.

Yevgeny Prighozin, ya musanta tuhumar da Amurka ke masa.

Amurka na ganin cewa shi ne mutumin da ya samar da kudade ga wata hukuma kasar Rasha mai suna Internet Research Agency - wadda saka dubban tallace-tallace a shafukan sada zumunta domin baza labaran kanzon kurege gabanin zabukan kasar Amurka.

Amurka kuma ta ce ta gan wasu laifukan na daban da Rashar ta aikata da suka hada da harin guba da aka kai kan wani dan leken asiri da 'yarsa a Birtaniya.

Labarai masu alaka