Mutum hudu sun mutu bayan da gada ta fada kan motoci

Emergency personnel works on a collapsed pedestrian bridge on the Florida International University in Miami, Florida. Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu, 10 kuma suka sami rauni bayan da wata gada ta rushe kusa da jami'ar Miami da ke jihar Florida.

Masu ceto na can na neman wadanda suka tsira da rayukansu, inda gadar ta fada kan motoci ta kuma danne su.

Gadar ta baude kuma ta fada kan wata babbar hanya mai daukar layin motoci takwas da yammacin Alhamis, inda jami'a n'yan sanda suka ce ta danne mtoci takwas.

Kawo yanzu babu cikakken bayanin yawan mutanen da ke karkashin gadar a lokacin da hatsarin ta auku.

An kai mutum 10 asibitin Kendall Medical Center, kuma mutum biyu na cikin mawuyacin hali, inji likita Mark McKenney, wanda shi ne bababn likitan fida a asibitin.

Hakkin mallakar hoto EPA

An gina gadar mai nauyin tan 950, kuma mai tsawon kafa 174 ne ranar Asabar da ta gabata cikin sa'o'i shida kacal, kamar yadda wani bayani ya nuna a shafin intanet na jami'ar.

Wadanda lamarin ya faru a gabansu sun ce an dakatar da motoci masu wucewa ne a daidai lokacin da gadar ta rushe gaba daya da misalin karfe 5:30 agogon GMT.

Labarai masu alaka