'Juyin mulki a ka yi min'- Mugabe

An kori Mugabe daga mulki ne a watan Nuwamban bara Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kori Mugabe daga mulki ne a watan Nuwamban bara

Tsohon Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya yi magana a karon farko tun bayan da a ka kore shi daga mulki a watan Nuwambar bara, inda ya ce juyin mulki a ka yi masa.

Mr Mugabe ya bayyanawa kafar yada labaran Afirka ta Kudu, cewar magajinsa Emmerson Mnangagwa ya zama Shugaban kasa ne kawai saboda goyon bayan rundunar sojan kasar da ya samu.

Mr Mugabe ya ce "ban taba tunanin wanda na baiwa kulawa, na jawo cikin gwamnati kuma wanda na dage wajen ceto rayuwarsa daga halaka zai zo wata rana ya juya min baya ba."

Mr Mugabe ya ce a shirye ya ke ya taka rawa wajen kawo sauyi a Zimbabwe sannan kuma ya yi sulhu da Mr Mnangagwa kan cire shi da a ka yi daga mulki ba a bisa ka'ida ba.

Labarai masu alaka