Faransa ta nemi a kama gimbiyar Saudiyya

A street sign of the Avenue Foch in the 16th sub-district of Paris (file photo) Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin wannan lamarin ya faru ne a wani masauki a wani yanki a Paris a watan Satumba 2016

Wani alkali a kasar Faransa ya bayar da izinin kama diyar sarkin Saudiyya Gimbiya Hassa bint Salman.

Ana zargin Gimbiya Hassa da umartar wani mai tsaronta ya doki wani ma'aikaci a masaukinta da ke Avenue Foch a birnin Paris.

Kafofin watsa labarai na Faransa sun ce wanda aka azabtar din ya ce ya dauki hoton dakin da ya kamata yi gyara, kuma ana zarginsa a kan yana son ya sayar da hotunan.

Tuni dama ana tuhumar mai tsaron nata da laifin wani abu makamancin wannan da ya faru a shekara ta 2016.

Kamfanin dillancin labarai na AFP sun shaida cewa wanda aka azabtar ya ce an naushe shi, an daure shi, kuma an tilasta masa ya sumbaci kafafun gimbiyar, kuma ba a bar shi ya bar masaukinta ba sai bayan sa'o'i.

An ruwaito cewa Gimbiya Hassa, wadda dan uwanta ne Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, ta tsere daga Faransa ba da jimawa ba bayan faruwar lamarin.

Labarai masu alaka

Karin bayani