Nigeria: Mutum miliyan 3.8 ba sa samun abinci - FAO

Bags of Indian rice Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahoton ya nuna cewa 'fiye da mutum miliyan 10 suna neman abin da za su ci, sannan fiye da miliyan 3.8 su na bukatar abinci da gaggawa

Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya tare da Shirin Samar da Abinci na Duniya WFP sun yi gargadi cewa karancin abinci zai shafi mutane miliyan 3.8 a jihohi 16 a arewacin Najeriya da Abuja, babban birnin kasar.

Sun bayyana hakan ne a lokacin da suka gabatar da sakamakon bincikensu na watan Maris din kan yanayin rashin abinci da ake ciki a kasar.

Jihohi 16 din sun hada da Bauchi da Benue da Gombe da Jigawa da Plateau da Niger da Kebbi da Katsina da Kaduna da Taraba da Sokoto da Kano da Yobe da Borno da kuma Adamawa.

Rahoton mai taken CH ya nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu a jihohi 16 da Abujan, fiye da mutum milayan 3.8 ba za su samu abinci ba kwata-kwata a tsakanin watannin Yuni da Agusta, saboda lokacin damuna ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahoton ya ce an shiga wannan halin nan ne saboda matsalolin Boko Haram da fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya

Rahoton ya nuna cewa 'fiye da mutum miliyan 10 suna neman abin da za su ci, sannan fiye da miliyan 3.8 su na bukatar abinci da gaggawa.

Ya kara da cewa wasu mutum fiye da miliyan 5.8 kuwa ba su da abinci kwata-kwata kuma ba su da hanyar samunsa, yayin da gidaje da dama suke da abincin ci na 'yan watanni kawai, saboda haka suna bukatar taimaikon gaggawa kafin abubuwa su karasa lalacewa.

Rahoton ya kuma nuna ce wa an shiga wannan halin nan ne saboda ba a samu isasshen amfanin gona ba a sama da shekaru uku, sakamakon matsalolin Boko Haram da fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

Labarai masu alaka

Karin bayani