Europa League: An hada Arsenal da CSKA Moscow

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal na son lashe kofin Europa domin shiga gasar zakarun Turai

Arsenal za ta hadu da CSKA Moscow ta Rasha a gasar zakarun Turai ta Europa League zagayen daf da na kusa da karshe

Arsenal ce za ta fara karbar bakuncin fafatawar a Emirates a ranar 5 ga Afrilu, kafin mako na gaba ta kai wa CSKA ziyara a Moscow.

Atletico Madrid ta biyu a teburin La liga za ta hadu ne da Sporting Lisbon ta Portugal.

RB Leipzig ta Jamus za ta hadu ne da Marseille, yayin da kuma aka hada Lazio ta Italiya da Salzburg ta Austria.

Arsenal dai ta tsallake ne bayan ta casa AC Milan da jimillar kwallaye 5-1 a fafatawar da suka yi gida da waje.

Wannan ne kuma karon farko da Arsenal ta kai zagayen daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai tun 2010.

Yanzu kuma babban kalubalen Arsenal shi ne lashe kofin gasar domin samun gurbi a gasar zakarun Turai a kaka ta gaba.

Maki 12 ne tsakanin Arsenal da matsayi na hudu a teburin Premier.

Sauran kungiyoyin da aka hada:

RB Leipzig da Marseille

Arsenal da CSKA Moscow

Atletico Madrid da Sporting Lisbon

Lazio da Red Bull Salzburg

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba