Haihuwa da rainon ciki a karkara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Haihuwa da rainon ciki a karkara

Ku latsa alamar hoton da ke sama don sauraron cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zahra Umar ta yi da wasu matan a karkara:

A wannan makon shirin Adikon Zamani ya yi duba kan irin wahalhalun da matan karkara ke fuskanta yayin goyon cikin da haihuwa.

A don haka ne muka yi tattaki zuwa garin Sandamu da ke jihar Katsina, kuma na gamsu da yadda na ga mata na kokarin yin abubuwa masu muhimmanci don ci gaban rayuwarsu duk da irin kalubalan da suke fuskanta.

Matan da muka hadu da su gwaraza ne da ke tsaye a kan kafafunsu duk da dumbin matsalolin yau da kulllum da rashin ababen more rayuwa.

Da dukkan alamu dai kauyukan da ke arewacin Najeriya ba su samu ci gaba ba tun shekarun 1960.

Har yanzu da hannu suke surfa tsabar da za su yi abinci, su daka, su girka da kara, sannan kuma su deebo ruwa a rijiya ko rafi.

Har yanzu a gida suke haihuwa ba tare da samun kulawar zamani ta likitoci ba.

Ga dukkan alamu dai gwamnatocinmu ba su mayar da hankali sosai ba don ci gaban kauyuka a shekarun nan, kuma hakan ya fi shafar mata kai tsaye.

Na hadu da wata matashiya wadda ta yi kaura daga wani babban gari zuwa kauye don kawai ta rayu da namijin da ta kamu da sonsa a waya! Labarinta na da matukar jan hankali.

Mai yiwuwa ne mu matan birni mu koyi wani abu daga matan karkara, kamar rike zumunci, da kyautatawa, saboda gaskiya mutanen kauye suna da kirki, ba munafunci sai aminci da yarda da juna.

Fatana shi ne mu hada hannu mu kyautata rayuwar mata da yaran da ke arewacin Najeriya.

Labarai masu alaka