Shin me Buhari ya fada wa shugabannin Majalisa?

Buhari da shugabannin majalisa Hakkin mallakar hoto @BashirAhmaad
Image caption Sen Bukola Saraki ya fadi dalilin da ya sa ba su amince da kasafin kudi ba

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wata ganawa ta musamman da shugabannin majalisun dokoki na kasar.

Ganawar tsakanin bangaren zartawa da majalisa ta samu halartar shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara.

Sai kuma wasu shugabannin majalisa da suka hada da mataimakin kakakin majalisar wakilai Lasun Yusuf da Sen Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila.

Babu dai cikakken bayani game da hakikanin abubuwan da aka tattauna yayin ganawar da aka yi a daren Alhamis.

Amma bayan kammala ganawar, shugaban majalisar dattawa Sen Bukola Saraki ya yi magana da 'yan jarida a madadin majalisa.

Sakataren gwamnati kuma Boss Mustapha ya yi magana a madadin bangaren zartawa.

Sun shaida wa manema labarai cewa batutuwan da aka tattauna sun hada da kasafin kudi da gyaran fuska ga dokokin zabe na kasa, da samar da ayyukan yi.

An yi ganawar ne a daidai lokacin da ake kai ruwa rana tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.

A kwanan nan ne shugaba Buhari ya yi watsi da kudirin gyara dokar zabe, duk da kudirin ya samu amincewar zauren majalisun Tarayya guda biyu.

'Yan majalisar kuma sun ce za su yi gaban kansu su amince da dokar duk da shugaban bai amince ba.

Sannan akwai batun kasafin kudi da majalisa ba ta amince da da shi.

Hakkin mallakar hoto @BashirAhmaad

Amma a yayin da yake zantawa da manema labarai, Bukola Saraki ya ce dalilin da ya sa ba su amince da kasafin kudin ba saboda wasu daga cikin hukumomin gwamnati ba su je sun kare kasafinsu ba.

Tun bayan gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa, shugaba Buhari ya bayar da umurni ga kowace ma'aikata ko hukumar gwamnati ta je gaban majalisa ta kare kasafin kudinta.

Da aka tambayi Bukuloa saraki ko sun tattauna kan batun sauya dokar zabe, sai ya ce ba su tattauna kan batun ba.

Amma wasu majiyoyi sun ce batun yana daga cikin abubuwan da aka tattauna a ganawar da shugabannin majalisar suka yi da Buhari.

Kudirin wanda majalisun biyu suka amince ya shafi sauya dokokin zaben Najeriya, ciki har da fara gudanar da zaben 'yan Majalisar Tarayya kafin na shugaban kasa.

Amma cikin wasikar watsi da kudirin da shugaba Buhari ya aika wa majalisar, ya ce kudirin ya saba wa 'yancin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke da alhakin shiryawa da gudanar da zaben, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.