Dokar zabe: Me ya sa Saraki da Dogara suka hade kai

Buhari da Saraki da Dogara Hakkin mallakar hoto @BashirAhmaad
Image caption An dade ana takun saka tsakanin bangaren majalisar da na zartarwa

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara sun bayyana matsayinsu kan batun sauya dokar zabe.

Shugabannin majalisun tarayyar guda biyu a Najeriya sun ce za su dauki mataki da murya daya.

Saraki da Dogara sun bayyana haka ne a cikin sanarwar hadin guiwa da masu magana da yawunsu suka rabawa manema labarai.

Sun fitar da sanarwar ne domin mayar da martani ga labarin da wasu jaridun Najeriya suka buga cewa an samu sabanin ra'ayi tsakanin Saraki da Dogara kan batun sauya dokar zabe.

A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya yi watsi da kudirin, a cikin wasikar da ya aikawa zauren majalisun tarayyar guda biyu.

Shugaban ya yi watsi da kudirin ne, duk da ya samu amincewar majalisun tarayyar guda biyu.

Sanarwar da shugabannin majalisar suka fitar ta ce "Muna son kowa ya sani cewa muna kan ra'ayi daya game da matakin da ya kamata mu dauka kan watsi da sauya dokar zabe da shugaba Buhari ya yi."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bukola Saraki da Yakubu Dogara za su dauki mataki guda kan sauya dokar zabe

Sanarwar ta kara da cewa, shugabannin majalisar sun tattauna kuma sun amince a kan matakin da ya kamata su dauka da yadda za su dauki matakin da lokaci da kuma dalilin daukar matakin.

Tuni dai 'Yan majalisar suka ce za su yi gaban kansu su amince da dokar duk da shugaban bai amince ba.

Sun ce ba wai don bukatarsu ba suke son a sauya dokokin zaben, illa don a inganta mulkin dimokuradiya.

Shugabannin majalisar kuma sun ce doka ta ba majalisa dama da 'yanci ta yi gyara ga dokokin.

Kudirin wanda majalisun biyu suka amince ya shafi sauya dokokin zaben Najeriya, ciki har da fara gudanar da zaben 'yan Majalisar Tarayya kafin na shugaban kasa.

Amma cikin wasikar watsi da kudirin da shugaba Buhari ya aika wa majalisar, ya ce kudirin ya saba wa 'yancin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke da alhakin shiryawa da gudanar da zaben, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.