Tasmeniya: Jihar da mata suka fi maza yawa a majalisa

Tasmania's opposition leader Rebecca White and her deputy, Michelle O'Byrne Hakkin mallakar hoto TASMANIA LABOR
Image caption Shugabar jam'iyyar adawa Rebecca White (hagu) tare da mataimakiyarta Michelle O'Byrne

Jihar Tasmeniya ta kafa tarihi a matsayin wadda ta zabi 'yan majalisa mata fiye da maza a karon farko.

Jihar ce mafi kankanta a cikin jihohin Ostreliya wadda ta gudanar da zabuka a ranar 3 ga watan Maris, amma sai a wannan makon aka kammala kidayar kuri'u.

Amma yankin babban birnin Ostreliya ma ya taba zaban mata a majalisar yankin da suka zarce maza a 2016, sai dai yankin ba jiha ba ne.

An zabi mata 13 da maza 12 a majalisar wakilai ta Tasmeniya. 'Yan siyasa daga jihar sun ce lamarin abin "alfahari ne kwarai".

"Yana nuni ga mata masu tasowa cewa akwai haske wajen cimma muradansu na siyasa," inji Michelle O'Byrne, wadda ita ce mataimakiyar shugabar jam'iyyar Labor masu adawa.

Amma a majalisar tarayyar Ostreliya, ba haka lamarin ya ke ba, inda kimanin kashi 70 cikin 100 na 'yan majalisar maza ne.

Labarai masu alaka