Zaben Rasha: Vladimir Putin ya sami gagarumar nasara

Vladimir Putin, President of Russia speaks during the Preliminary Draw of the 2018 FIFA World Cup in Russia at The Konstantin Palace on July 25, 2015 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Putin ya shafe kusan shekara 20 yana mulkin Rasha

Vladimir Putin zai cigaba da mulkin Rasha na wasu shekaru shida bayan da ya lashe zaben shugaban kasa a karo na hudu.

Bayan da aka kusan kammala kididigan kuri'un da aka kada, alkaluma sun nuna ya sami kashi 76 cikin dari kamar yadda hukumar zabe ta kasar ta wallafa.

An dai hana babban mai adawa da Mista Putin, Alexei Navalny daga tsayawa takara a wannan zaben.

Bayan da aka bayyana wani bangare daga cikin sakamakon zaben, Mista Putin gaya wa magoya bayansa cewa masu kada kuri'a "sun fahimci tasirin cigaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan".

Ya kuma fada wa manema labarai cewa ba zai cigaba da neman shugabancin kasar ba har illa ma sha Allah:

"Wannan abin dariya ne. Kana ganin zan cigaba da zama a nan har sai na kai shakara 100 da haihuwa? Ina!"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bayan da aka bayyana wani bangare na sakamakon zaben, Mista Putin ya gana da magoya bayansa

Labarai masu alaka