'Kungiyar IS ce ta sace 'yan matan Dapchi'

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne aka sace 'yan mata 110 daga makarantar Dapchi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar 19 ga watan Fabrairu ne aka sace 'yan mata 110 daga makarantar Dapchi

Bangaren kungiyar Boko Haram da ke mubaya'a da kungiyar masu fafutika ta IS ne ya sace 'yan makarantar sakandare ta Dapchi a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kafar yada labarai ta Amurka ta Wall Street Journal, WSJ, ta ce ta samu bayanan da suka tabbatar mata da cewa bangaren Abu Musab Abu Musab al-Barnawine suka sace 'yan matan 110 a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Da ma dai an dade ana rade-radin cewa mayakan Abu Musab al-Barnawi, wanda suke kiran kansu reshen IS na Afirka ta Yamma, su ne da alhakin lamarin.

Sace 'yan matan na Dapchi na zuwa ne shekara hudu bayan da Boko Haram karkashin jagorancin Abubukar Shekau suka sace sama da 'yan mata 200 daga garin Chibok.

Editan WSJ a Afirka ya yi ta wallafa jerin karin bayanai kan rahoton a shafinsa na Twitter:

Sakon yana cewa: "Sabon rahotonmu kan sace 'yan matan Dapchi ya bayyana abubuwa da dama kan yakin basasar da ke kunshe cikin Boko Haram". Ga bayanan da za ku karanta:

Ya kara da cewa: "Wani bangare na kuniyar IS karkashin jagorancin Abu Musab al-Barnawi ba bangaren Abubakar Shekau ba, su ne suka sace yaran Dapchi.

Rahoton ya bayyana cewa shugaban kungiya mai alaka da IS din Abu Musab al-Barnawi, shi ne dan marigayi Muhammad Yusuf, tsohon jagora, kuma mutumin da ya kafa kungiyar ta Boko Haram.

WSJ ta ce shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ya nesanta kansa da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, kuma yana fuskantar matsin lamba daga kungiyar da ta balle din.

Rahoton ya ce a watan Agustar 2016 kungiyoyin biyu sun yi arangama da juna, abun da ya jawo mutuwar mayakansu 400.

Rahoton dai ya kuma ce an fara tattaunawar sirri domin kubutar da 'yan matan na Dapchi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai tattauna da wadanda suka sace 'yan matan don ceto su.

Labarai masu alaka