Na'urorin Amurka za su maye gurbin ma'aikatan Afirka

Motocin da na'ura ta samar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kirkiri fasaha domin gudanar da wasu ayyukan da ya kamata mutum ya yi

Wani sabon rahoto ya yi gargadin cewa cikin kasa da shekara 20 nan gaba zai fi sauki da arha a yi amfani da na'ura a masana'antun Amurka maimakon a yi hayar ma'aikatan da za su yi aiki a Afirka.

An kirkiri fasaha domin gudanar da wasu ayyukan da ya kamata mutum ya yi, kuma suna aiki ba tare da taimakon mutum ba.

An yi hasashen cewa faduwar farashin na'urorin za su jawo rashin ayyukan yi a yayin da masu kamfanoni za su koma kasashen da suka fi karfin tattalin arziki.

Wasu masu sharhi sun ce wannan zai fi shafar kananan kasashe, ko da yake cibiyar nazarin ci gaban kasashen waje (ODI) na ganin ba haka ba ne.

Rahoton da cibiyar ta fitar ya nuna cewa kasashen Afrika suna da damar da za su rungumi sabon sauyin.

"Kasashen Afrika ba za su yi wasa ba a harakar masana'antu, kuma maimakon haka za su inganta hanyar samun damar intanet da zuba jari ga fannin fasaha da kirkire-kirkire," a cewar Karishma Banga, babban jami'in bincike a cibiyar ODI.

Ya kara da cewa: "Idan har aka yi da kyau, fasaha dama ce ga kasashen Afrika wajen samar da ayyukan yi a masana'antu."

Ana ganin sauyin ba zai shafi kananan kasashe ba saboda ba su da kudin da za su saka jari a fannin ci gaban fasahar.

"Bincikenmu ya nuna cewa wannan ya wuce kima. A yanzu kudaden tafiyar da na'urorin ya fi tsada idan aka kwatanta da lebaranci, amma wannan ba zai kasance ba a cikin shekaru 15," kamar yadda Dirk Willem te Velde daraktan ODI ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Rahoton ODI ya gano cewa sauya tsarin tafiyar da ayyukan sarrafa katako zuwa kujeru da sauransu a Afrika zuwa ta hanyar Intanet ya fi arha a Amurka fiye da kudaden da ake samu na lebaranci a Kenya daga shekarar 2034.

A Habasha kuma zai fi sauki tsakanin 2038 zuwa 2042.

Rahoton ya ce wannan dama ce ga Afrika ta fara gina tunaninta tsakanin shekaru 10 zuwa 20 a fannonin fasaha da suka shafi abinci da tufafi.

Rahoton ya kuma ba kasashen Afrika shawara su inganta wadatuwar intanet da bunkasa ayyukan hannu ta hanyar bayar da horo tare da mayar da hankali kan darussan ci gaban fasaha a makarantun Ilimi na Afrika.

Labarai masu alaka

Karin bayani