Yaushe za a doke Barcelona a La Liga?

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallo 13 kawai ta shiga ragar Barcelona a La Liga a bana

Akwai yiyuwar Barcelona na iya kafa tarihi a bana a gasar La Liga ta Spain, a matsayin kungiya ta farko da ta buga dukkanin wasannin gasar ba tare da an doke ta ba.

Barcelona ta ci gaba da kare matsayinta na daya a kakar bana bayan ta doke Athletic Bilbao da ci 2-0 karawar mako na 29 da suka yi a ranar Lahadi.

Kuma yanzu Barcelona ta buga wasa 29 ba tare da an doke ta ba a liga a kakar bana, wasa 36 idan aka hada da kakar ta gabata.

Rabon da a doke Barcelona a lig tun a watan Afrilun bara da ta sha kashi a gidan Malaga da ci 2-0.

Barca ta ci gaba da zama ta daya a kan tebur da maki 75, tazarar maki 11 tsakaninta da Atletico Madrid wacce ta sha kashi a hannun Villarreal da ci 2-1 a ranar Lahadi.

Sau daya aka samu galabar Barcelona a bana a dukkanin wasa 45 da ta buga.

Espanyol ce ta doke ta a karawar farko da suka fafata a gasar Copa del Ray zagayen daf da na kusa da karshe, amma Barcelona ce ta yi waje da ita a karawa ta biyu.

Babu dai wani Kulub a tarihi da ya buga wasanni 38 ba tare da an doke shi ba a La Liga.

Real Sociedad ce ta taba buga wasanni 32 ba tare da an doke ta ba a kakar 1979-80.

Yanzu wasa tara ne ya rage a kammala gasar lig, kuma Barcelona ta ci 23, ta yi canjaras shida a wasa.

Hakazalika kwallo 13 kawai aka zura musu a wasa 29 na lig, yayin da kuma suka ci kwallo 74.

Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce ya fi kaunar ya kammala La liga ba tare da an doke shi ba, da ace ya lashe kofuna uku da Barcelona ke hari a bana.

"Za mu yi kokarin lashe sauran wasannin da suka rage," a cewar kocin, wanda wannan ce kakarsa ta farko a kulob din.

Yanzu Barcelona na jiran buga wasan karshe ne tsakaninta da Sevilla a gasar Copa del Ray ranar 21 ga watan Afrilu, a yayin da ta ke harin lashe kofin La liga karo na 25.

Sannan ana ganin Barcelona na iya kai wa zagayen kusa da karshe bayan an hada ta da Roma a gasar zakarun Turai.

Sai dai duk da cewa wasa tara ne ya rage a kammala La liga, wasu na ganin akwai kalubale a gaban Barcelona.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi ya ci kwallo 25 a La Ligar bana

Daga cikin manyan wasannin da za su kasance kalubale ga Barcelona sun hada da karawar da za ta yi tattaki zuwa Sevilla a ranar Asabar din karshen mako mai zuwa.

Da karawa da Valencia a ranar 15 ga Afrilu da haduwar Barcelona da Celta Vigo a ranar 18 ga Afrilu.

Sannan akwai karawar hamayya ta Clasico da Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a Nou Camp a ranar shida ga watan Mayu.

A karawar farko da suka yi a watan Disamba, Barcelona ce ta doke Madrid da ci 3-0 a Santiago Bernabeu.

Labarai masu alaka