Manufar yarjejeniyar kasuwancin bai-daya a Afirka

Rwanda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasashen Afrika sun fi huldar kasuwanci da Turai da Asiya.

A ranar Talata ne ake bude taron shugabannin Tarayyar Afirka inda ake sa ran za su sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya.

Sai dai za a gudanar da taron ne ba tare da Najeriya ba, ta biyu a karfin tattalin arziki a Afirka, bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar da kauracewa taron da za a gudanar a Rwanda.

Wasu na ganin kasancewar Najeriya a taron yana da matukar amfani, saboda matsayin tattalin arzikinta a Afirka, kamar yadda wasu ke ganin amincewa da yarjejeniyar zai bunkasa kasuwanci da samar da dubban ayyukan yi.

Wasu kuma na bayyana shakku ne game da sharudda da kuma yadda za a aiwatar da yarjejeniyar kasuwancin ta bai-daya tsakanin kasashen na Afirka.

An dade ana tattauna yadda za a kulla yarjejeniyar, kusan shekaru da dama.

A karkashin yarjejeniyar, dukkanin kasashen Afirka 54 za su amince su rage harajin shigo da kayayyaki da nufin bunkasa kasuwanci tsakaninsu.

Wannan dai shi ne matakin farko ga samar da hadin guiwar fadada tattalin arziki tsakanin kasashen.

Hakazalika, ana bukatar ko wacce kasa ya kasance ta amince babu harajin shigo da kayayyaki ko kuma babu wani banbanci ga tsarin harajinta na shigo da kayayyaki da sauran kasashen.

Daga nan za a kulla kasuwanci na bai-daya, inda za a yi cinikin kayayyaki kyauta tsakanin kasashen tare da hada kai domin karfafa dangantakar kasuwanci da sauran kasashen duniya.

Karin hadin kan kuma ya kunshi na siyasa da samar da kudin bai-daya.

Wakilin BBC da ke aiko da rahotanni kan kasuwanci a Afirka Matthew Davies ya ce wadannan bukatun sun dauki kungiyar Tarayyar Turai fiye da shekaru 50 kafin a kafa bayan kammala yakin duniya na biyu.

Ko da yake an samu wanzuwar irin wannan hadin kan a Afirka, kamar kungiyar kasashen gabashin Afirka da kuma ta yammacin Afirka ECOWAS.

Amma ga dorewar kasuwancin bai-daya, dole sai ya kasance an gudanar da mafi yawancin kasuwancin tsakanin kasashen Afirka.

Wakilin BBC ya ce wannan shi ne babban kalubalen da za a fuskanta, domin yawancin kasashen Afirka sun fi hulda ne da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afirka bai wuce kashi 16 ba duka. A tsakaninsu da kasashen yankin Asiya kuma kashi 51, a Turai kuma adadin ya kai kashi 70.

Hakan ya nuna yana da wahala yarjejeniyar kasuwancin ta bai-daya karbu cikin lokaci kankani.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Najeriya sai ta yi nazari kan alfanu da ribar yarjejeniyar kafin ta shiga

Wani babban kalubalen shi ne girman Afirka, musamman yawan kasashen da za su sanya hannu a kan yarjejeniyar.

A lokacin da aka fara a Turai a 1950, kasashe shida ne kawai suka sanya hannu, sai bayan shekaru sama 60 kafin Tarayyar Turai ta samu mambobi 28.

Afirka kuma yanzu tana da kasashe 54, ko da yake yanzu Najeriya ta fice.

Yanayin kasuwancin bai-daya a irin yanki na Afirka babban jan aiki ne.

Amma idan matakan farko da aka bi na neman hadin kan tattalin arziki ne da bunkasa cinikayyya a Afirka, to ba mamaki mutanen nahiyar za su amfana.

Labarai masu alaka