Obasanjo dalibi ne mai bin doka - Farfesa Abdalla

Olusegun Obasanjo da Farfesa Abdallah Hakkin mallakar hoto NOU
Image caption Lokacin da Cif Obasanjo (na biyu daga dama) ya halarci bikin kammala karatunsa

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya nuna hazaka da bin doka da oda a lokacin da yake karatu a budaddiyar jami'ar kasar wato National Open University, acewar shugaban jami'ar.

Farfesa Abdalla Uba Adamu shaida wa BBC cewa, a lokacin da Cif Obasanjo, ke karatu a wannan jami'a, ya kiyaye duk wasu dokoki da ka'idojinta kamar yadda sauran dalibai ke yi.

Mista Obasanjo ya kasance daya daga cikin dalibai sama da 14,000 da aka ya ye daga jami'ar.

Tsohon shugaban ya kammala digirin digirgir ne wato dokta a ilmin addinin Kirista, kuma a farkon bana ne ya karbi shaidar karatunsa.

A shekarar 2001 ne Mista Obasanjo ya farfado da jami'ar a lokacin da ya ke mulki, bayan rufetan da aka yi a 1984, amma ba ta fara aiki ba sai a shekarar 2003/2004.

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya ce idan an bayar da irin aikin nan da ake yi a gida wato 'assignment' a Turance, Obasanjo "bai taba fashin kawo na sa ba".

Sannan kuma Obasanjo ya bukaci malaman da suke koyar da shi da su rinka adalci a karatunsu, inda ya ce musu kada su yi la'akari da girmansa ko matsayinsa ace za a raga masa.

Ya ce a rinka yi masa "duk abin da ake yi wa sauran dalibai domin shi ma a sahunsu ya ke".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Obasanjo ya ce ya yi digirin digirgir ne saboda sha'awar da ya ke da ita ta neman ilimi

Farfesa Abdallah, ya ce karatun da Obasanjo ya yi a wannan jami'a, darasi ne ga sauran jama'a, musamman matasa, inda ya nuna cewa tsufa ba ya hana karatu.

Dama dai Cif Obasanjo, ya dauki alkawarin kasancewa daya daga cikin daliban da za a yaye a jami'ar.

Tsohon shugaban Najeriyar ya ce ya yi wannan karatu ne saboda sha'awar da ya ke da ita a bangaren ilimi.

Karanta karin wasu labaran

Labarai masu alaka