An nada dan shekara 16 kwamishina amma...

Faysal Abdullahi Omar Hakkin mallakar hoto Faysal Abdullahi Omar
Image caption Omar ya ce ya shafe kwanaki ba ya zuwa makaranta tun bayan aika masa da takardar nada shi kan mukamin

Wani matashi dan shekara 16 ya yi watsi da tayin mukamin mataimakin kwamishinan wata jiha a kasar Somalia saboda rashin tsaro.

Ana sa ran Faysal Abdullahi Omar zai fara aiki a Jowhar, babban birnin Hirshabelle na Kudu maso Gabashin kasar.

Sai dai dan makarantar ya shaida wa BBC cewa yana tsoron karbar mukamin zai iya sa mayakan al-Shabab su far masa.

Kungiyar masu tayar da kayar bayan dai na da karfi a yankin.

Omar ya ce ba a tuntube shi ba kafin a sanar da sunansa, wanda shugabannin kabila ne ke yi a kasar, a don haka yana so ya mayar da hankali kan karatunsa.

"A yanzu ina karatu a babbar sakandare kuma nan ba da jimawa ba zan kammala, ina so na tafi jami'a domin gina rayuwata ta gaba," kamar yadda ya shaida wa sashin Somaliya na BBC.

Ya kara da cewa ya shafe kwanaki ba ya zuwa makaranta tun bayan aika masa da takardar nada shi kan mukamin.

Iyayen Omar sun nuna damuwa kan nadin nasa. Sai dai ya ce wasu jama'a a yankin sun shaida masa cewa wata dama ce ta zamowa "abin koyi ga matasa".

Ya ce "na hadu da mutane da dama da suka nemi na karbi wannan aiki".

Birnin Jowhar yana arewacin Mogadishu, babban birnin kasar, kuma yana da karkashin ikon gwamnatin Somalia.

Kungiyar al-Shabab ce ke iko da yankunan da ke makwaftaka da yankin.

A 'yan makonnin da suka wuce masu tayar da kayar baya sun kashe wani dan majalisa a yankin.

Labarai masu alaka

Karin bayani