An umurci 'yan sandan Nigeria su janye daga gadin masu kudi

Sufeton 'yan Sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto NPF
Image caption An sha bayar da umurnin amma ana yin watsi da shi

Babban sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayar da umurnin janye dukkanin jami'an 'yan sanda da ke tsaron manyan mutane da kamfanoni.

Ya ce an dauki matakin ne saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kasar.

Jami'an 'yan sanda kimanin 150,000 aka bayyana cewa suna gadin masu kudi da jami'an gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da babban sufeton 'yan sandan na Najeriya ke bayar da umurnim janye jami'an 'yan sandan daga aikin tsaron gidajen manyan mutane ba.

Sai dai sau da dama, ana yin watsi da umurnin.

A wani taron da ya gudanar tare da manyan jami'an 'yan sanda, sufeto janar na 'yan sandan Ibrahim Idris, ya ce wajibi ne kwamishinonin 'yan sandan jihohin Najeriya su mutunta umurnin cikin gaggawa.

Ya ce hakan ya zamo tilas saboda yadda rayuwar mutanen Najeriya miliyan 200 ke fuskantar barazanar kalubale na tsaro.

Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashi.

Hakazalika, rikici tsakanin makiyaya da manoma na ci gaba da zama barazana a yankin tsakiya da arewa maso yammacin Najeriya.

Sannan ana fama da rikicin kabilanci da sace-sacen jama'a da fashi da makami a sassan kasar da kuma rikicin masu fafutikar kafa kasar Biafra a kudu masu gabashi.

Masana na ganin tura 'yan sanda domin gadin wasu tsirarun mutane, a yayin da rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya ke cikin barazana ya nuna sakaci ga aikinsu na kare rayukan jama'a.

Labarai masu alaka