An kama tsohon shugaban Faransa saboda 'karbar' kudin Gaddafi

Ex-French President Nicolas Sarkozy (L) with Gaddafi in Libya in Tripoli, 25 Jul 2007 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana zargin Sarkozy da karbar makudan kudade daga wajen Gaddafi don yakin neman zabe

'Yan sanda sun kama tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy don yi masa tambayoyi kan zargin da ake masa na karbar makudan kudi don yakin neman zabensa, daga wajen tsohon Shugaban Libya Muammar Gaddafi.

'Yan sanda suna bincike kan zargin rashin bin tsari kan samar da kudaden aiwatar da yakin neman zaben shugaban kasa da ya yi a shekarar 2007.

A baya 'yan sanda sun yi masa tambayoyi kan wannan bincike. Sai dai Mista Sarkozy ya yi watsi da aikata ba daidai ba.

Tsohon shugaban kasar dai mai matsakaicin ra'ayi bai samu damar komawa kujerar mulki ba a 2012.

Majiyoyin shari'a sun ce ana yi masa tambayoyin ne a Nanterre, wani yanki da ke wajen yammacin birnin Paris.

A 2013 ne Faransa ta fara wani bincike kan zarge-zargen cewa ya karbi kudade sosai daga wajen Gaddafi don yakin neman zabe.

Majiyoyin sun ce 'yan sanda sun kuma yi wa daya daga cikin tsoffin ministocin Mista Sarkozy kuma na hannun damansa Brice Hortefeux, tambayoyi a ranar Talata.

Ko za a gurfanar da Mr Sarkozy a gaban kuliya?

Har yanzu binciken bai kai wannan matakin ba.

Yana hannun 'yan sanda don yi masa tambayoyi inda za a rike shi ne kawai na tsawon sa'a 48.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nicolas Sarkozy ya musanta aikata ba daidai ba

Kafofin watsa labaran Faransa sun ce wannan ne karo na farko da 'yan sanda suka tsare shi kan zargin karbar kudi daga Gaddafin.

Amma an taba tsare shi a 2014 a wani binciken na daban kan zargin yin bushasha da kudaden neman zabe.

Wadanne zarge-zarge ake yi kan wannan batun?

A watan Nuwambar 2016, Ziad Takieddine ya shaida wa kafar yada labaran Faransa ta intenet, mediapart cewa a tsakanin 2006-2007 ya bai wa Mista Sarkozy da shugaban ma'aikatansa Claude Guéant akwatuna uku cike da takardun kudin euro 'yan 200 da 'yan 500.

Mr Takieddine ya yi zargin cewa kudaden sun fito ne daga hannun Gaddafi kuma yawansu ya kai Yuro miliyan biyar, daidai da dala 6.2.

A wannan lokacin Mr Guéant ne ke tafiyar da harkokin yakin neman zaben Mr Sarkozy.

An taba bincikensa a farkon shekarar nan kan wani kudi da ya aike ta banki kimanin Yuro 500,000 a 2008. Ya yi watsi da aikata ba daidai ba, ya kuma ce ya samu kudin ne ta hanyar sayar da wasu zanensa guda biyu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ziad Takieddine ya ce ya bai wa mataimakan Sarkozy kudi lakadan da Gaddafi ya bayar

Jaridar Faransa Le Monde ta rawaito cewa Bashir Saleh, wanda shi ke kula da asusun tara kudade na musamman na Libya a wancan lokacin, ya tabbatar da cewa Gaddafi ne ya bai wa Sarkozy kudin domin yakin neman zabe.

Tuhume-tuhumen da ake sa ran za a yi musu kan wannan batu sun hada da amfani da tasirinsa da zamba da ajiye kadarorin sata da halatta kudin haram.

Wadanne bincike kuma a ke wa Sarkozy?

An umarci Mr Sarkozy ya fuskanci kuliya a wata shari'ar ta daban da ake zarginsa da amfani da kudade don yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba.

Ana zarginsa da cewa ya yi zamba wajen kara yawan kudin yakin neman zabe a 2012, wanda yawansa ya kai Yuro miliyan 22.5.

Mr Sarkozy ya karyata cewa ya wuce gona da iri wajen kashe kudin.

Labarai masu alaka

Karin bayani