Matsalar tsabtataccan ruwan sha ta karu a duniya

Matsalar ruwan sha Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani rahoton Bankin Duniya ya ce yawan mutanen da ke rayuwa ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba sun karu.

Rahoton da Bankin Duniya ya fitar albarkacin ranar Ruwa ta duniya ya ce yawan mutanen da ba su da tsabtataccen ruwan sha a duniya sun kai miliyan dubu dari takwas da arba'in da hudu.

Rahoton ya ce mutum guda cikin tara a duniya na rayuwa ne ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba.

Binciken ya yi nazari ne kan yawan mutanen da suke samun tsabtataccen ruwan sha a gida ko kuma suke da halin samun ruwan a kasa da sa'a daya.

Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da aka ware domin bikin ranar ruwa ta duniya da nufin wayar da kan al'umma game da muhimmancin tsaftataccen ruwan sha.

Bankin Duniya ya yi kira ga 'yan siyasa da su tashi tsaye domin tunkasar matsalar, kamar yadda rahoton ya ce: "Idan ba ruwa mai tsabta sauran bukatu na duniya da suka danganci kiwon lafiya da ilimi da kuma daidaiton jinsi ba za su samu ba.

Rahoton kuma ya ce matsalar ta fi muni a Afrika.

Kazalika rahoton ya yi gargadin ce cewa gwamnatoci da dama a nahiyar Afirka babu wani abin azo a gani da suke wajen samar da tsabtataccan ruwan sha, abinda ke jefa rayukan miliyoyin mutane cikin hadari.

Sai dai a India da China ne rahoton ya ce yawan mutanen suka fi yawa, amma idan aka yi la'akari da yawan jama'a, matsalar ta fi tsanani a Afrika, musamman a kasashen Eritrea da Uganda da Habasha da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo da kuma Somalia.

A Najeriya ma dai ana fuskantar matsalar rashin ruwa mai tsafta, kuma rashin ruwa da muhalli mai tsaftar na haddasa mutuwar yaran da ba su kai shekara biyar ba a kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jama'ar yankunan karkara a Najeriya sukan dogara ne da gurbataccen ruwa daga tafkuna.

Rahoton na Bankin Duniya ya ce yara 'yan kasa da shekaru biyar kimani dubu tamanin ke mutuwa duk rana a duniya sakamakon cututtuka da suka shafi matsalar tsabattaccen ruwan sha.

Masharhanta dai na ganin batun cimma burin samar da ruwan sha mai tsabta da kuma wadatarsa a kasashen duniya wani babban kalubale ne ga hukumomi.

Labarai masu alaka