Malami ya danganta maman daliba da kankana a India

Daliban sun yi zanga-zangar ne rike da kankana a hannayensu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban sun yi zanga-zangar ne rike da kankana a hannayensu

Daliban wata kwaleji a jihar Kerala da ke kudancin kasar India, sun gudanar da zanga-zanga, bayan wani malami a makarantar ya danganta maman wata daliba da kankana.

An watsa hoton bidiyon da aka dauka a lokacin da malamin ke fada wa dalibar wannan kalma a kafafan sada zumunta a cikin karshen makon daya gabata, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kai, inda mutane ke ta mayar da martani a fusace, musamman mata.

Wannan hoton bidiyo da aka sanya a kafafan sada zumuntar, shi ya har zuka wasu dalibai inda suka bi tituna, hannayensu kuma rike da kankanar da aka yayyanka suna zanga-zangar kin amincewa da irin wadannan kalamai ga mata.

Malamin dai farfesa ne, wanda ke koyarwa a kwaleji horarwa ta Farook da ke Kerala, ya kuma fada wa dalibar kalmar ne saboda yanayin shigar da ta yi inda ta bar kirjinta a waje, da kuma wasu sassa na jikinta.

Wannan shiga da dalibar ta yi ne ya fusata farfesan, saboda ya ga kamar ba ta yi shigar mutunci ba, shi ya sa ya ce mata, mamanta kamar kankana.

Wata kungiyar kare hakkin matasa a jihar, ta ce ba za ta lamunci cin zarafin mata ta hanyar fada musu duk maganar da aka ga dama ba.

Duk wani yunkuri da manema labarai suka yi don jin ta bakin hukumar gudanarwar kwalejin ko kuma malamin a kan wannan batu, ta ci tura.

Labarai masu alaka