An ci zarafin ma'aikacin BBC a Lagos

BBC ta ce ba za ta lamunci cin zarafin duk wani ma'aikacinta ba
Image caption BBC ta ce ba za ta lamunci cin zarafin duk wani ma'aikacinta ba

BBC ta yi alawadai da wulakancin da wasu jami'an gwamnatin Lagos suka yi wa ma'aikacinta ta hanyar kwace masa kayan aikinsa ta karfin tsiya tare da goge dukkan hotunan da ya nada na wani aikin korar mutane daga wani waje a jihar.

An gudanar da aikin korar mutanen ne a wani wajen gyaran motoci wanda aka ajiye daruruwan motoci da sauran kayayyakin lantarki na miliyoyin dalloli.

Wajen dai na kusa da inda ake zubar da sharar data mamaye yankin Ojota a jihar ta Lagos..

Masu sana'a a wajen, sun nuna damuwa a kan shirin gwamnatin jihar ta Lagos na rufe wajen kafin a ba su inda za su ci gaba da gudanar da sana'arsu.

Gwamnatin jihar dai ta ce tulin sharar da ke kusa da wajen, na da matukar illa ga lafiya, shi ya sa ma ta ke bukatar wadanda suke gudanar da kasuwanci ko kuma ke zaune a wajen da su bari.

Ma'aikacin BBCn wanda ke aiki a shahen Yarabanci, Joshua Ajayi, ya ziyarci wajen ne domin tattaunawa da wadanda ke zaune a wajen, gabanin a rufe wajen kwata-kwata, lnda anan ne jami'an gwamnatin suka farmasa tare da kwace masa wayarsa ta salula.

Tawagar jami'an gwamnatin su shida wanda wani mataimakin darakta a ma'aikatar kula da muhalli ta jihar ke jagoranta, ta yi barazanar kama ma'aikacin BBCn, bayan da ya bukaci su bashi wayar salularsa.

Daga bisani dai an bashi wayarsa, amma kuma an goge wasu hotunan bidiyo da sauran muhimman abubuwan da ke cikin wayar.

Babban sakatare a ma'aikatar dai bai bayyana dalilin da ya sa aka kwace kayan aikin dan jaridar ba da kuma dalilin goge masa wasu muhimman abubuwa ba.

BBC ta ce, sam ba ta ji dadin abinda ya faru ba, kuma zata nemi karin bayani daga mahukuntan jihar a kan dalilin da ya sa aka yi wa ma'aikacinta haka.

Daga nan ta bukaci gwamnatin jihar ta Lagos, da ta rinka kyale ma'aikatanta na gudanar da aikinsu yadda yakamata ba tare da an yi mata katsalandan ba, saboda dukkan ma'aikatanta sun san ka'idar aikinsu da kuma abin da yakamata su yi da ma wanda bai dace suyi ba.

To sai dai kuma tuni kwamishinan ma'aikatar kare muhalli na jihar, Babatunde Durosimi--Etti, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce ya nemi afuwa a kan abinda ya faru, sannan ya ce, za su yi nazari a kan abinda ya faru".

Kafin faruwar lamarin dai wakilin BBCn, ya zanta da wadanda ke zaune a wajen da za a rushen inda suka shaida masa cewa kafin a fara rusau din, sai da suka wakilta wasu a cikinsu domin su gana da jami'an ma'aikatar kula da muhallin, amma sa'oi kadan bayan dawowarsu, sai kawai ba zato ba tsammani suka ga an fara rufe musu shagunansu ba tare da an ce ga wajen da zasu koma ba.