'Yan matan sakandaren Dapchi '104 aka sako'

Wani mahaifin 'yar makarantar Dapchi na share hawayen murnar sakin matan Hakkin mallakar hoto ISAAC LINUS ABRAK
Image caption Wani mahaifin 'yar makarantar Dapchi na share hawayen murnar sakin matan

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan matan sakandaren Dapchi 104 kungiyar Boko Haram ta sako da kuma wani yaro da yarinya daya.

Yanzu jimilla 106 da aka sace, Boko Haram ta sako a safiyar Laraba.

Wata sanarwa da ofishin ministan watsa labaran kasar, Lai Mohammed, ya fitar ta ce an sako matan ne tare da taimakon "wasu kasashe abokan Najeriya ba tare da an sanya wani sharadi ba."

Sanarwar, wacce kakakin ministan, Segun Adeyemi, ya aike wa manema ta kara da cewa "umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa dukkan jami'an tsaro domin su tabbatar da sako 'yan matan makarantar Dapchi, wadanda aka sace ranar 19 ga watan Fabrairun 2018, ya soma yin nasara, inda ranar Laraba aka saki 104 daga cikin 110 da aka sace."

A cewar Lai Mohammed, gwamnati na ci gaba da kokarin ganin an sako sauran wadanda ake garkuwa da su

Ya kara da cewa jami'an tsaro sun dakatar da gudanar da ayyukansu a yankin domin tabbatar da cewa ba a rasa rai ba lokacin da ake komawa da matan gida.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An mika wa gwamnatin Tarayya 'yan Matan zuwa Abuja

"Gwamnati ta fahimci cewa rikici da taho-mu-gama ba su ne mafita ba domin kuwa za su iya zama silar salwantar rayukan wadannan matan, don haka ne kuma zabi bin hanyar lumana," in ji Mr Mohammed.

Iyayen 'yan matan sun ce an sako 'ya'yan nasu da safiyar Laraba.

Mahaifin daya daga cikin 'yan matan, Kundili Bukar, ya gaya wa BBC cewa wasu mutane da ake tsammani 'yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci.

A cewarsa, sun ajiye su ne kawai suka tafi kuma 'yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Daya daga cikin iyayen 'yan matan ya shaida wa BBC cewa kungiyar Boko Haram ta rike daya daga cikin 'yan matan sannan biyu sun mutu.

Sai dai sanarwar da Lai mohammed ya fitar ba ta yi tsokaci kan matan da suka mutu ba.

Abin da ya faru tun sace 'yan Matan

Hakkin mallakar hoto GGSS
 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

A nasa bangaren, ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ya shaida wa manema labaria cewa ba a biya kudin fansa gabanin sako 'yan matan ba, ko da yake babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Matan na Dapchi na hannun hukumar leken asiri ta farin kaya kuma nan gaba a ranar Laraba ne jami'an hukumar za su yi wa Shugaba Buhari da 'yan kasar bayani game da sakin matan, a cewar fadar shugaban kasar.

A watan jiya aka sace matan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.

A wancan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani bala'i da ya shafi kasar baki daya.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka