BBC ta kaddamar da babban ofishin Afrika ta yamma a Lagos

BBC Yoruba

BBC ta kaddamar da sashen Afrika ta yamma a birnin Lagos na Najeriya, wanda ya kunshi manyan harsunan kasar guda hudu.

Bikin kaddamar da sashen na zuwa bayan BBC ta bude sassa biyu na harsunan Igbo da Yoruba a ranar 19 ga Fabrairun da ya gabata.

A bara ne kuma BBC ta bude sashen Pidgin a Lagos, domin mutanen da ke magana da turancin buroka.

Yanzu sabon sashen na yammacin Afrika ya kunshi sashen Hausa da Yoruba da Igbo da kuma Pidgin, duka a Najeriya.

Sabbin sassan da sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar, ya kasance shirinsa mafi girma tun shekarun 1940, sakamakon kudin da gwamnatin Birtaniya ta bai wa sashen a shekarar 2016.

Amma sabbin rassan Igbo da Yoruba da Pidgin za su watsa labaransu ne ta intanet.

An shirya gagarumin biki a Lagos domin kaddamar da reshen na Afrika ta yamma.

Bikin zai kunshi manyan masu ruwa da tsaki a BBC da suka hada da Jamie Angus daraktan watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC.

Sannan an gayyaci manyan mutane da fitattu a fannin kare harshe da kuma al'adu.

An kirkiri shafin #BBCWAfricalaunch a twitter ga wadanda ke son bibiyar lamurran shagalin bikin.

A shekarar 2015 ne gwamnatin Birtaniya ta sanar da ware wasu kudade don sake inganta ayyukan da BBC ke yi a duniya, wanda hakan ya sanya aka samu karin harasan da ya kamata a bude a Afirka da kuma yankin Asiya.

Labarai masu alaka