APC da fadar shugaban Nigeria ne suka kitsa sace matan Dapchi

PDP Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan Dapchi 110 a watan jiya.

Wata sanarwa da kakakin PDP Kola Ologbondinyan ya aike wa manema labarai ta ce APC da wasu jami'an fadar shugaban kasar ne suka shirya sace matan "domin cimma wani buri na siyasa."

A cewar sanarwar, "Jam'iyyarmu na ganin hakan a matsayin mugunta da rashin mutunci da kuma izgilanci inda aka yi amfani da 'yan matan makarantar da ba su ji ba ba su gani ba domin shirya wasan kwaikwayon da aka yi na yaudarar 'yan Najeriya, duk domin a sake zabensu a 2019."

PDP ta ce wannan abu ne da ba za a taba yafewa ba.

Sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da wannan zargi na PDP.

"Mutanen Najeriya na sace cewa an aikata wannan mummunan aiki ne domin yaudarar jama'a... a kirkiro wani yanayi da zai nuna cewa gwamnatin APC ta yi rawar gani sannan Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da burinsa na sake tsayawa takara a zaben 2019, watakila cikin makonni masu zuwa," in ji PDP.

A ranar Laraba ne wasu mutane da ake tsammani 'yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci.

Mahaifin daya daga cikin 'yan matan, Kundili Bukar, ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram sun sauke matan ne kawai suka tafi kuma 'yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan matan sakandaren Dapchi 101 kungiyar Boko Haram ta sako.

Wata sanarwa da ofishin ministan watsa labaran kasar, Lai Mohammed, ya fitar ta ce an sako matan ne tare da taimakon "wasu kasashe abokan Najeriya ba tare da an sanya wani sharadi ba."

A cewar Lai Mohammed, gwamnati na ci gaba da kokarin ganin an sako sauran.

Image caption Satar 'yan matan ta jawo ce-ce-ku-ce

Abin da ya faru tun sace 'yan Matan

Hakkin mallakar hoto GGSS
 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

Yadda aka sace 'yan matan

Daya daga cikin 'yan matan ta shaida wa BBC yadda aka sace su:

"Muna zaune a cikin dakunanmu sai muka ji kara, da farko mun dauka cewa na'urar raba wutar lantarki ce ta fashe, sai muka ji karar ta ci gaba.

Sai suka shigo dakananmu, inda muka yi kokarin ficewa ta kofar baya amma sai suka sha kanmu suka zuba mu motoci.

A kan hanyar tafiya ne biyar daga cikinmu suka mutu.

Daga nan sai suka kaimu wani wuri inda muka kwana sannan suka sa muka dafa abinci muka ci.

Sai suka kara tafiya da mu wani wurin daban.

Sun rinka kula da mu suna ba mu abinci da ruwan sha, ba su yi mana komai ba".

Da aka tambaye ta ko za ta koma makaranta sai ta ce:

"A'a. Sun shaida mana cewa ka da mu ci gaba da karatun boko".

Labarai masu alaka