Kasashe 44 sun sanya hannu kan kasuwancin bai-daya a Afrika

Taron kasuwancin bai-daya a Afrika Hakkin mallakar hoto AFP

Kasashen Afrika 44 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya wacce aka tsara da nufin cinikayya ba haraji tsakanin kasashen.

An bayyana cewa yarjejeniyar da ake kira ACFTA za ta samar da kasuwa ga mutanen Afrika sama da biliyan.

Sai dai kuma rahotanni daga Rwanda inda ake gudanar da taron sun ce kasashe 27 kawai ne suka amince a shigar da fitar da kaya ba tare da wani shamaki ba a iyakokin kasashen.

Bukatar kasashen da ke goyon bayan kulla yarjejeniyar shi ne shigar da kayayyyaki da ba mutane 'yancin izinin shiga domin aiki a kasashen na Afrika.

A karkashin yarjejeniyar, dukkanin kasashen da suka sanya hannu za su rage harajin shigo da kayayyaki da nufin bunkasa kasuwanci tsakaninsu.

Tun kafin sanya hannu a yarjejeniyar ne dai ta fuskanci cikas inda Najeriya ta biyu a karfin tattalin arzikin Afrika ta janye.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta ce sai ta kara nazari kafin ta sanya hannu a yarjejeniyar.

Masana tattalin arziki na ganin kudirin kasuwancin na bai-daya a Afrika zai taimaka wajen magance matsalar rashin ayyukan yi tsakanin matasa a nahiyar.

Kuma suna ganin akwai kalubale da dama da za a fuskanta a gaba kafin fara cin moriyar yarjejeniyar.

Babban kalubalen shi ne yadda yawancin kasashen Afirka ke dogaro da huldar kasuwanci da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Misali kamar Najeriya da ke samar da manja, amma kuma yawancin kasashen Afrika sun fi gwammacewa su shigo da shi daga kasashen yankin Asiya da Turai.

Labarai masu alaka