Najeriya ta ce 'kyauta Boko Haram ta sako 'yan matan Dapchi

Dapchi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mahaifin 'yar makarantar Dapchi na share hawayen murnar sakin matan

Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta biya kudin fansa domin a saki 'yan Matan makarantar sakandaren garin Dapchi da Boko Haram ta sace.

Wata sanarwa da ofishin ministan watsa labaran kasar, Lai Mohammed, ya fitar ta ce babu wani musayar fursuna da aka yi domin sakin 'yan matan.

Sanarwar ta kara da cewa yanzu jimillar mutane 106 aka sako wadanda aka sace a Dapchi da suka hada da dalibai 'yan mata 104 da kuma wani yaro da yarinya daya.

"Rahotannin da suka ce an biya kudin fansa ba gaskiya ba ne," a cewar Lai Mohammed.

Ya ce an mika ma su 'yan matan da wani yaro daya, wato tawagar gwamnatin Tarayya ta mutane hudu da suka isa Maiduguri domin rako 'yan matan zuwa Abuja.

Tawagar ta kunshi ministan cikin gida Janar Danbazau da Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ministan harakokin waje da kuma Hon. Goni Lawan Bukar, dan majalisa da ke wakiltar Dapchi.

An dauki 'yan matan zuwa Abuja a cikin wani jirgin soji daga Maiduguri.

Yadda aka sace 'yan matan

Daya daga cikin 'yan matan ta shaida wa BBC yadda aka sace su:

"Muna zaune a cikin dakunanmu sai muka ji kara, da farko mun dauka cewa na'urar raba wutar lantarki ce ta fashe, sai muka ji karar ta ci gaba.

Sai suka shigo dakananmu, inda muka yi kokarin ficewa ta kofar baya amma sai suka sha kanmu suka zuba mu motoci.

A kan hanyar tafiya ne biyar daga cikinmu suka mutu.

Daga nan sai suka kaimu wani wuri inda muka kwana sannan suka sa muka dafa abinci muka ci.

Sai suka kara tafiya da mu wani wurin daban.

Sun rinka kula da mu suna ba mu abinci da ruwan sha, ba su yi mana komai ba".

Da aka tambaye ta ko za ta koma makaranta sai ta ce:

"A'a. Sun shaida mana cewa ka da mu ci gaba da karatun boko".

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin Sojoji ya dauki 'yan Matan zuwa Abuja daga Maiduguri

Abin da ya faru tun sace 'yan Matan

 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan Dapchi 110 a watan jiya.

Wata sanarwa da kakakin PDP Kola Ologbondinyan ya aike wa manema labarai ta ce APC da wasu jami'an fadar shugaban kasar ne suka shirya sace matan "domin cimma wani buri na siyasa."

Sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da wannan zargi na PDP.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka