Hotunan bikin bude ofishin BBC na Afirka Ta Yamma a Lagos

Ga wasu zababbun hotuna na bikin kaddamar da sabon ofishin BBC a Afirka Ta Yamma da ke birnin Lagos a kudu maso yammacin Najeriya.

BBC ta kaddamar da sashen Afirka ta yamma a birnin Lagos na Najeriya, wanda ya kunshi manyan harsunan kasar guda hudu.

Hakkin mallakar hoto Google

Mutane dada kabilun kasar daban-daban sun halarci kaddamar da katafaren ofishin da yake unguwar Ikoyi a babban birnin kasuwancin Najeriya.

Bikin kaddamar da sashen na zuwa bayan BBC ta bude sassa biyu na harsunan Igbo da Yoruba a ranar 19 ga Fabrairun da ya gabata.

A bara ne kuma BBC ta bude sashen Pidgin a Lagos, domin mutanen da ke magana da turancin buroka.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan al'amuran watsa Malam garba Shehu ya samu halartar bikin, tare da tsohon editan sashen Hausa na BBC Mansur Liman.

Yanzu sabon sashen na yammacin Afirka ya kunshi sashen Hausa da Yoruba da Igbo da kuma Pidgin, duka a Najeriya.

Image caption Peter Okwoche da Bilkisu Labaran suna gabatar da tsare-tsaren bikin

Sabbin sassan da sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar, ya kasance shirinsa mafi girma tun shekarun 1940, sakamakon kudin da gwamnatin Birtaniya ta bai wa sashen a shekarar 2016.

An shirya gagarumin biki a Lagos domin kaddamar da reshen na Afirka ta yamma.

Daga kasa hoton tawagar ma'aikatan sashen Hausa na BBC ne da suka halarci kaddamar da ofishin.

Daga hagu Halima Umar Saleh ce, sai Aliyu Tanko da Jimeh Saleh editan BBC Hausa, da Isah Sunusi tsohon ma'aikacin BBC da Naziru Mika'ilu da Haruna Tangaza, da Farima Othman da Ummulkhairi Saleh (masu hidimar kasa), da Yusuf Ibrahim Yakasai da Abdussalam Usman Abdulkadir da kuma wakilinmu na Lagos Umar Shehu Elleman.

Labarai masu alaka