Syria: Za a kwashe 'yan tawaye daga Ghouta

Yakin da ake tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Syria, ya lalata garin Ghouta Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Yakin da ake tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Syria, ya lalata garin Ghouta

Nan gaba kadan ne daruruwan mayakan 'yan tawayen Syria tare da iyalansu, za su fara barin garin Ghouta da ke gabashin Syria wanda aka yi wa kawanya a karkashin wata yarjejeniya da Rasha ta shirya.

Rahotanni sun ce, mayakan 'yan tawayen sun amince su ajiye makamansu domin a basu dama su koma lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar ta Syria, inda 'yan tawayen ke rike dashi.

Idan hakan ta tabbata, to zai zama aikin kwashe 'yan tawayen na farko daga Gabashin Ghouta, wanda ya fuskanci munanan hare-hare daga bangaren dakarun gwamnatin kasar tun a watan da ya gabata.

An yanke garin Harasta daga sauran sassan gabashin Ghouta.

Kungiyar 'yan tawaye ta Ahrar al Sham, ce dai ke rike da shi, inda yanzu aka tabbatar da cewa ta amince ta dai na yaki, sannan kuma za su bar wajen.

Akwai irin wannan yarjejeniyar da ake tattaunawa da wasu manyan kungiyoyin 'yan tawaye biyu a yankin, wato kungiyar 'yan tawaye ta Jaish al Islam da Faylaq al Rahman, amma kuma har yanzu ba a cimma komai ba.

Dukkannin kungiyoyin biyu sun sha alwashin ci gaba da da yaki duk da cewa ana ta kora su.

Kazalika har yanzu ana harba makaman roka a Damascus, inda dakarun gwamnati ke rike da shi.

Wani hari da aka kai ranar Talatar da ta wuce, shi ne mafi muni a baya-bayan nan, inda aka hallaka mutum fiye da 40.

Dabarun da dakarun gwamnatin kasar keyi na yi wa waje kawanya da kuma ruwan bama-bamai, ta sa an samu muhimmiyar nasara, to sai dai kuma duk da haka, an yi asarar rayuka da yawa a cikin shekarun baya-bayan nan.

Irin wannan yanayi dai, shi ke faruwa a gabashin Ghouta, inda dubban fararen hula suka kasance ba su da wani zabi illa su bar gidajensu, sannan kuma ko su mika kansu ko kuma a hallaka su.

Labarai masu alaka