An daure 'yar Palasdinu don ta mari sojan Isra'ila

Ahed Tamini ta isa kotun da aka yanke mata hukunci ne sanye da kayan fursunoni Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ahed Tamini ta isa kotun da aka yanke mata hukunci ne sanye da kayan fursunoni

An yanke wa wata matashiya 'yar kasar Palasdinu mai kimanin shekara 17, hukuncin zaman gidan kaso na tsawon wata takwas, saboda ta mari wani sojan Isra'ila.

Wannan lamari dai ya ja hankalin mutane da dama a sassan duniya bayan da aka wallafa hoton lamarin a kafar intanet, inda aka nuna Ahed Tamini, ta tunkari sojojin a kofar gidanta a watan Disambar da ya gabata.

An sanya wa Ahed Tamini, ankwa a kafarta, inda kuma ta ke sanye da kayan da fursunoni ke sanyawa a lokacin da ake tafiya da ita zuwa wata kotun soji.

Bayan isar su kotun, ta daga wa 'yan uwanta hannu tare da cewa ba bu adalci a wannan aiki na shari'a.

Yarinyar dai ta amince da wata yarjejeniyar amsa laifi, wadda a karkashinta za a zartar mata da daurin watanni takwas a gidan yari.

Kafofin yada labarai na Isra'ila sun ce, an rage tuhume-tuhumen da ake yi wa Ahed Tamimi, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da ke bukatar amincewar kotun soja.

Kazalika yarinyar, ta zama wata alama ta gwagwarmayar Palasdinawa, an kuma dauki hotonta ne a kofar gidansu ta na kalubalantar wasu sojojin Isra'ila biyu masu dauke da makamai.

Yawancin 'yan kasar Isra'ila sun goyi bayan sojojin inda suke ganin laifin yarinyar, tare kuma da zargin iyayenta da goyon bayanta, suna masu cewa an sha kyaleta a lokuta da dama ta na tsigale sojojin Isra'ilan.

Labarai masu alaka