Amurka ta sanya dokar hakar mai a Sudan ta Kudu

Yakin basasar kasar ya faro ne bayan shugaba Salva Kiir ya kori mataimakinsa Riek Machar
Image caption Kashi 93 cikin 100 na kasafin kudin Sudan ta Kudu ya dogara ne ga man fetur

Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanin mai a Sudan ta Kudu, a wani mataki na hana yadda kudaden da ake samu ke rura wutar yakin basasa a kasar ta Sudan ta Kudu.

Amurka ta ce daga yanzu Amurka da sauran kamfanoni za su bukaci lasisi na musamman gabanin samun fasaha ko kayan aiki ga wasu kwamfanonin mai sha biyar, da hukumomin gwamnati.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta kasar tace gwamnatin Sylva Kiir wacce ta bayyana a matsayin gungun 'yan cin hanci da rashawa.

Amurkar ta kara da cewa suna amfani da kudaden mai wajen sayar makamai, da bawa 'yan bindiga dadi makamai, da kuma yin kafar ungulu ga zaman lafiya. A watan jiya Amurka ta sanyawa Sudan ta Kudu takunkumin sayen makamai.

Labarai masu alaka