Mutanen da suka kashe Musulmi za su sha daurin rai da rai a India

Volunteers of the vigilante group of Gau Raksha Dal (Cow Protection Squad) gather to inspect a truck on a highway in Taranagar in the desert state of Rajasthan. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai kungiyoyi da dama da ke sa ido kan masu safarar shanu a India

Wata kotun jihar Jharkhand da ke India ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan mutum 11 saboda samunsu da hannu kan kisan wani Musulmi mai tallan naman shanu a bara.

Mutanen sun lakadawa Alimuddin Ansari, mai shekara 55, dukan tsiya har sai da ya mutu saboda yana safarar naman shanu.

Wannan ne karon farko da kotun India ta daure mutanen da ke sanya ido kan masu cin naman shanu, duk da cewa an kwashe shekara da shekaru ana kai hari kan Musulmin da ke sayar da naman.

Mabiya addinin Hindu na kallon saniya a matsayin wata halitta mai tsarki kuma an haramta kisanta a jihohi da dama na kasar, ciki har da jihar Jharkhand.

Sau da dama masu sanya ido kan masu cin naman shanu suna kai hari kan maciya naman shanun da masu sayar da shi a India, kuma ko da 'yan sadan sun yi bincike ba safai suke hukunta mutane ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani