Biciken da ake yi min ya sanya ni cikin kuncin rayuwa — Sarkozy

Former French President Nicolas Sarkozy enters his car as he leaves his house in Paris, 21 March 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Sarkozy ya ce ana zarginsa ba tare da kwakkwarar hujja ba

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya ce zarge-zargen da ke yi masa cewa ya karbi tallafin kudi daga wurin tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi domin yin yakin neman zabe sun sa yana ji tamkar yana rayuwa a "jahannama".

Mr Sarkozy ya shaida wa wata kotun majistiret cewa "Ana zargi na ba tare da wata kwakkwarar hujja ba"a lokacin da ake bincikensa, in ji jaridar Le Figaro.

Ana bincikensa ne kan karbar kudin da suka haramta domin yakin neman zaben 2007, da kashe kudin kasar Libya ba bisa ka'ida ba da kuma cin hanci.

Mr Sarkozy, mai shekara 63, ya musanta aikata laifi.

Dan siyasar, wanda aka sallama ranar Laraba bayan an kwashe kwana biyu ana yi masa tambayoyi, ya ce masu zarginsa daga Libya na yin hakan ne domin yin ramuwar gayya saboda matakin da ya dauka na aikawa da jiragen yakin Faransa lokacin boren da ya yi sanadin tumbuke Gaddafi daga kan mulki a 2011.

'Yan sanda sun yi tambayoyi ga daya daga cikin tsofaffin ministoci kuma na hannun daman Mr Sarkozy, Brice Hortefeux, ranar Talata.

Ranar Alhamis, Le Figaro ta wallafa cikakken bayanin da ta ce Mr Sarkozy ya yi wa masu bincike na Faransa cikin harshen Faransanci.

A cikin bayanin, ya ce yana sane cewa zarge-zargen da ake yi masa "manya" ne, amma ana yi masa ne kawai domin a "bata" masa suna kuma hakan ya sa yana ji kamar yana rayuwa cikin jahannama tun 11 ga watan Maris din 2011, lokacin da Gaddafi ya yi zargin karon farko.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Sarkozy ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Libya da Faransa a 2007

I

Labarai masu alaka