Shugaba Buhari ya yi jaje ga mutanen Zamfara

Shugaban ya jajantawa 'yan jihar ta Zamfara saboda hare-haren 'yan fashin shanu Hakkin mallakar hoto NUJ
Image caption Shugaban ya jajantawa 'yan jihar ta Zamfara saboda hare-haren 'yan fashin shanu

Shugaban Najeriya Muhammadu ya ziyarci a jihar Zamfara da ke arewacin kasar ranar Alhamis.

Ya je jihar ne a ci gaba da ziyarar da yake kai wa jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro.

Shugaban ya jajantawa 'yan jihar ta Zamfara saboda hare-haren 'yan fashin shanu da suke fama da su.

A makon jiya ne shugaban na Najeriya ya kai ziyara jihohin Taraba, Benue da Yobe wadanda ke fuskantar kabulaben tsaro.

Wasu na zargin ziyarar na da nasaba da siyasa ganin cewa zabe na karatowa kuma an dade ana kashe-kashen bai je ba. Sai dai gwamnati ta musanta zargin.

Shugaban ya gana da sarakuna da shugabannin yankuna daban-daban da kuma masu ruwa da tsaki na jihar.

Jihar Zamfara na fuskantar kalubalen rashin tsaro a baya bayan nan.

Ko da a watan jiya sai da Shugaba Buhari ya bayar da umurnin gaggauta tura sojoji zuwa jihar bayan wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.

Hakkin mallakar hoto BUHARI SALLAU
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya samu tarbar jami'an gwamnati

Wani dan majalisar dattawan Najeriya da ke wakiltar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya yi zargin cewa gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya san 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar amma ya ki daukar mataki a kansu.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan zargi ba shi da kanshin gaskiya.

A farkon watan nan gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe Buharin Daji, mutumin da ake zargi da jagorantar barayin shanun da suka addabi jihar da hare-hare.

Labarai masu alaka